Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkakakken Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabin karshe, Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da sahabbansa da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya ku ‘yan uwa na masu girma, masu albarka, masu daraja, lallai mu sani, Manzon Allah (SAW) ya kasance mai gayar tawali’u, mai gayar kankan da kai. Yazo a cikin tarihinsa cewa, saboda gayar tawali’unsa, mafi yawan lokuta shi yake yiwa kansa hidima, kuma yakan taimaka wa iyalinsa a cikin ayyuka na yau da kullum na cikin gida. Akwai ma wani Sahabinsa da yake cewa, sun je kasuwa tare da Manzon Allah (SAW), sai yayi sayayya, sai yayi nufin ya rike masa abin da ya saya din, sai Manzon Allah (SAW) yace, a’a, sai dai ya rike da kansa. Har yake ce masa ma’abocin abu shi yafi cancanta da ya dauki abinsa. Haka nan yazo a kan cewa, akwai lokacin da Annabi (SAW) ya ziyarci Sahabinsa mai suna Sa’ad Dan Ubadah, da zai koma sai ya kawo dabba domin Manzon Allah (SAW) ya hau, sai ya hada shi da dan sa mai suna Qais domin ya raka shi.
Sai Manzon Allah ya hau dabbar yace wa Qais din ya hawo. Sai Qais din yace, a’a. Sai Manzon Allah (SAW) yace masa ko dai ya hawo, ko ya koma. Wato saboda Manzon Allah (SAW) ba ya son ya kasance shi yana tafiya kan dabba alhali shi kuma Qais yana bin sa a kasa. Wannan shi ma ya nuna tawali’u na Manzon Allah (SAW).
Akwai wani lokacin da suna cikin tafiya da Abdullahi Dan Abbas, sai ya kasance yana tafiya a bayansa, sai Manzon Allah (SAW) yace masa yazo daura da shi, sai abin yayi wa Abdullahi Dan Abbas nauyi, amma kasantuwar ya ga haka Manzon Allah (SAW) yake so, sai yazo daura da shi din suka ci gaba da tafiya, wanda shi ma wannan yana alamta muna tawali’un Manzon Allah (SAW).
Akwai lokacin da Manzon Allah (SAW) yayi tafiya shi da wasu Sahabbansa, sai suka bukatu da su yanka dabba, sai wani cikinsu yace shi zai yanka dabbar, wani yace shi zai yi fida, wani kuma yace shi zai daddatsa ta, sai Manzon (SAW) yace; “Ni kuma zan nemo itacen da za’a dafa naman.” Mu dubi irin wannan tawali’u na Manzon Allah (S’AW). Akwai misalai da dama na tawali’unsa (SAW) ta fuskoki daban-daban, da lokaci ba zai bani damar kawo wa ba.
Ya ku jama’ah, wallahi Annabi (SAW) ba ya raina kowa. Ba ya wulakanta Dan Adam, sannan yana ba wa kowa girmansa da hakkinsa. Lallai da ace mutanen duniya za su yi koyi da tawali’un Manzon Allah (SAW), to da duniya ta zauna lafiya da taimakon Allah!
Sannan Manzon Allah (SAW) ya kasance bai taba cewa da mai yi masa hidima don me kayi kaza ba, sai dai yace; da kayi kaza da yafi.
Annabi (SAW) yana kiran kowa da kinayarsa domin girmamawa, yana sanya kinaya ga marasa kinaya, yana bawa wanda ya shigo wurinsa da matashinsa, idan kuwa yaki amincewa sai ya rarrashe shi har sai ya karba.
Manzon Allah (SAW) yana fitowa bayan bullowar rana, domin yanayin addu’a ne tsakanin alfijir da bullowar rana. Sannan idan ya shiga gida sai ya zauna a farkon wurin da ya samu a kowa.
Abun tambaya anan shine, shin don Allah yanzu haka muke? Shin don Allah muna yin koyi da Manzon Allah (SAW) a halayensa da tawali’un? Ya Allah, ka ba mu ikon yin koyi da halaye irin na Manzon Allah (SAW), amin.
Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, kar mu zamanto marasa tawali’u, kar mu zamanto masu girman kai, kar mu zamanto masu raina bayin Allah ko masu wulakanta su saboda Allah ya bamu ilimi, kudi ko mukami. Mu sani, komai kudin ka, komai ilimin ka, haka ko wane irin mukami kake dashi, wallahi idan ka mutu ba’a rufe ka da ko kwabo. A yau kana iya sa shaddar dubu dari, amma da zaran ka mutu, da yadin dari biyu za’a rufe ka dashi. Ka mallaki bene hawa bakwai, amma idan ka mutu kabarinka bai wuce tsawon kafa biyu. Jikin nan naka da kake ta faman yiwa kwalliya, ka sani, da zarar ka mutu zai zamo abincin tsutsa ne. Komai kyawon halittar ka sai ka rube kamar yadda abinci ke rubewa ya zamo datti.
Kuma munin halittar ka ba yasa ayi maka likkafani dabam da na saura, wai don kadan ji sassauci.
Komai ilimi, kudi, mulki, karfi ko sarautarka, ba yasa a kara maka koda dakika idan kwanan ka ya kare. Komai dabarar ka sai ka mutu, don haka ‘yan uwa, mu rinka ganin darajar junanmu, kada mu bari duniya ta shagaltar damu har mu kai ranar da wani zai yi muna wanka sabanin kan mu, wani yasa muna tufafi sabanin kan mu, wani yayi muna tsarki sabanin kan mu, mu kasance a saman kafafun mu maimakon tafiya da kafafun wani, don ita duniya ba madawwama bace, don haka komai dadin kasuwa dole ta watse haka ma komai dadin duniya dole mu bar ta, ko muna so ko bamu so. Fatan mu shine, Allah yasa mu lashe jarrabawar duniya kamar lomar tuwo. Amin.
Ya Allah muna rokon ka, don tsarkin Sunayen ka, don so da kaunar da muke yiwa Manzon ka (SAW), Ya Allahu, Ya Rahmanu, Ya Hayyu, Ya Qayyumu, Ya Zal Jalali Wal Ikram, Ya Allah, muna tawassuli da ibadar da muke yi maka ta azumin wannan wata na Ramadan, Ya Allah ka kawo wa al’ummar Jihohin Zamfara da Kano, da dukkanin Jihohin Najeriya, da dukkanin ‘yan Najeriya baki daya dauki na musamman daga wurinka. Ya Allah, mun tuba, mun tuba, mun tuba, ka karbi tuban mu, ka gafarta muna, ka yafe muna, ka jikan mu, ka tausaya muna, ka dauke muna wannan jarabawa, ka yaye muna wannan musiba ta wannan annobar cutar coronavirus.
Ya Allah, mun yarda, mun amince, mun yi ikirari, cewa mu masu laifi ne, mu masu zunubi ne, mu ba kowa bane, mu masu rauni ne, Ya Allah, mun saba maka, mun kauce hanya, mun yi ba daidai ba, mun ki bin umurninka, Ya Allah ka tausaya muna, ka yaye muna wannan cuta ta annobar covid-19. Ya Allah, bamu da karfi, bamu da wayo, bamu da dabara, ina rokon ka, duk wanda ka jaraba da wannan cuta ta wannan sabuwar annoba, ya Allah, ka yaye masa ita. Ya Allah, duk wanda ka saukar wa wannan ibtila’i a gare shi, Ya Allah, ka warkar da shi. Ya Allah, duk Musulmin da suka rasu a cikin wannan jarabawa, Ya Allah duk wadanda ka karbi ran su sanadiyyar wannan cuta, Ya Allah, ka jikan su, ka yafe masu, ka haskaka kabarinsu, ka karbi shahadarsu, kayi masu sakamako da Aljannah Firdausi. Ya Allah, ka ba wa iyalansu, da ‘yan uwansu, da abokan arziki hakurin jure wannan rashi, amin.
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.