A cikin subul-da-bakan zancen da ya fita soshiyal midiya ta hanyar wasan ‘video game’, dan wasan Manchester City, Sergio Aguero ya gulmata shirin barin Barcelona da Leonel Messi ke yi a karshen kakar wasa mai zuwa.
Messi wanda tun barin sa kungiyar ta yarinta ya ke wasa a Barcelona tsawon rayuwar sa, an yi zaton duk da sabat-ta-juyattar da ake yi da shi tsawon watanni biyar kenan, zai daure ya yi ritaya a Barcelona.
Sauyawar Al’amurra:
Tsawon watanni kenan Messi ya rika kallon cewa ya fi kowa tasiri a kulob din. Wannan kuwa ya yi amfani da damar da ya samu yadda Shugaban Kulob din Josep Maria Bartomeu ya kasa kafa kan sa da karfi da yajin fada-a-ji a kulob din, kamar yadda shuhaban Real Madrid Florentina Perez ya kafu, ta yadda ko Rpnaldo bai isa ya yi masa kallon banza ba.
Shi kuwa Messi a yanzu hatta Bartomeu da sabon kociya Quique Sten duk kallon biyu-ahu ya ke yi musu.
Salsalar Sabani Da Messi:
Harka ta fara yin tsami ne lokacin da Barcelona ta rika shan dukan wulakanci a lokacin tsohon kociya Enesto Valvade, musamman a Champions League, har ta kai aka shi.
Shi kuma Daraktan Wasanni, kuma tsohon dan wasan bayan Barcelona, Erick Abidel, ya shiga twitter ya nuna cewa kusan laifin na ‘yan wasa ne, ba su tsayawa su na taka leda bakin-rai-bakin-fama.
Haushin wannan kalami na Abidal ya sa Messi ya kasa daurewa, ya shiga shafin sa ta Twitter, shi ma ya yi raga-raga da Abidal, tsohon dan wasan da sun buga wasa tare da Messi a kulob din.
Zafin Annobar Coronavirus:
Wannan ma ta kara kawo sabani sosai tsakanin Messi da Barcelona, yayin da Messi ya yi riga-malam-masallacin shiga twitter ya yi korafi akan zabge musu alawus da kulob din ya ce zai yi. Barcelona ta ji haushin yadda Messi ya yi azarbabin fitar da bayanan, tun ma kafin sashen watsa labaran kulob din ya kai ga yin sanarwa.
Halin Ba Ni Na Iya: Da yawa a Barcelona sun fara jin cewa Messi ya fara gundurar su, ganin yadda ya rika yin kane-kane ya na hura wutar a sayo sabbin ‘yan wasa, kuma ya rika yin kici-kicin din lallai sai wadanda ya ke so za a sayo, don haka ba za a sayo wadanda ba su kwanta masa a rai ba.
Wannan da kuma yadda Messi ke yi yawan jajircewa a kowace shekara sai an kara masa alawus da albashi, ya fara isar kungiyar, musamman a wannan yanayi da Coronavirus ta yi wa Spain raga-raga.
Matsalar Messi Da Wasu ‘Yan Wasa
Ganin yadda Messi ya fara zama wani gagararre a Barcelona, sai ya fara samun takun-saka da ‘yan wasa irin su Frenkie de Jong tun a wasan sa ba farko a matsayin sa ba sabon dan wasa a Barcelona, da irin su Marc Andre Ter-Stegen da kuma shugaban kulob Bartomeu.
‘Yan asalin kasar Faransa da ke wasa a kulob din irin su Antoine Griezman, Ousman Dembele da Samuel Umtiti sun ki yarda Messi ya maida su rakumi-da-akala. Kuma suka samu goyon baya daga Bartomeu.
Josep Bartomeu ya yi yunkurin saida Lius Suarez domin ya sayo Lautaro Martinez da Timo Werner, amma abin ya ci tura.
Kokarin maye gurbin Suarez da Aubameyang daga Arsenal ya ci tura bayan da Messi ya nuna rashin goyon baya. Sannan shi kuma Aubameyang ya ce ba zai je Barcelona ba sai sun sayar da Suarez, gudun kada ya je kulob din ya rika zaman benci a daidai lokacin da ya ke shirin fara gangara daga tasirin sa a wasan kwallon kafa a duniya.
Tirka-tirkar shirin Messi barin Barcelona dai ya mamaye jaridun duniya, ciki har da The Nation ta Najeriya.
A nasa bangaren, Aguero ya fita ya ce Messi zai ci gaba da wasa a Barcelona har kakar wasa mai zuwa. Mutane da dama dai na ganin cewa Aguero bai iya nade tabarmar kunya ba.
Discussion about this post