Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya janye batun maida almajirai jihohin su na asali, sannan ya rusa kwamitin da ya nada domin haka.
Hakan ya biyo bayan ganawa da yayi da wasu jiga-jigan malamai ne a jihar.
Idan ba a manta ba Gwamna Matawalle, kamar wasu gwamnonin ya lashi takobin maida almajirai jihohin su na asali a dalilin barkewa annobar Korona.
Sai dai kuma yanzu ya canja shawara, ya ce duk wanda ke son yin almajirci a jihar Zamfara, ya garzayo abin sa, gwamnati na maraba da shi.
” Abin da za muyi maimakon maida su, shi ne za mu inganta salon karatun yayi daidai da na zamani.
Kamar yadda Kakakin gwamnan ya fadi, Matawalle ya ce ” Ba za mu maida almajirai ko daya jihar sa ta asali ba. Wadanda kuma aka maida jihohin su ma za su iya zuwa Zamfara, su ci gaba da zama muna maraba da su.
” Na janye maida su jihohin su na asali da kuma yin maraba da duk almajirin da ke so ya zo jihar ne saboda rage musu radadin kyamatar su da ake yi da kuma kyamatar salon karantar da yara na almajirci da ake yi yanzu.
Ya ce kowanne almajiri na da ikon zama da walwala a kowanni jiha a fadin Kasar nan ba tare da an muzguna masa ko an nuna masa wariya ko an kyamace ba. Saboda haka wadanda aka kora a wasu jihohin ma muna maraba da su a jihar Zamfara.