Wasu masu fama da cutar Coronavirus da aka killace a Cibiyar Killacewa ta Kwanar Dawaki, sun rufe kofa suka hana wasu likitoci biyu da nas daya fita daga dakin da suke a killace.
Tsohon Shugaban Kungiyar Likitocin Jihar Kano ne, Aminu Mohammad ya shaida wa Gidan Radiyon Wazobia FM, a ranar Juma’a, a wata hira da suka yi da shi cikin wani shiri da ake yi da ‘broken English.”
Mohammed ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da likitocin suka je domin aikin dubiyar masu cutar.
Ya ce masu cutar sun kulle likitocin biyu da nas daya har tsawon sa’o’i hudu, suka hana su fita, har sai da suka kusa kasa maida numfashi, saboda dukkanin su na sanye da rigunan kariyar da suka rufe musu jiki rub.
Ya ce sun ceci rayukan su ne yayin da suka yi kumumuwa, suka karya kyauren kofar suka fice da tsiya.
Sai dai kuma a lokacin da ake tattaunawar, wani majiyyaci daga cibiyar killacewar, wanda su ne suka hana su fita, ya kira tashar radiyon kai-tsaye ya karyata likitan cewa ba da tsiya suka fita ba, kuma ba su karya kofa ba.
“Jami’in kula da cibiyar ne, wanda dama akwai makulli a hannun sa, shi ne ya zo ya bude su suka fita.” Inji majiyyacin wanda ya ji bayyana sunan sa.
Ya kara da cewa sun rufe likitocin sun hana su fita ne domin su nuna bacin ran rashin kulawar da ake yi musu.
“Akwai rashin abincin kirki kuma akwai rashin kulawa. Idan aka dauki jini sai a yi kwanaki bakwai ba a kawo maka sakamako ba, ballantana ka ga shin ka warke ko ba ka warke ba. Sai ka yi sama da sati biyu kwance, ko da ka warke ba za ka sani ba, ka na kwance cikin masu cutar, saboda an dauki gwajin jinin ka amma ba a kawo maka sakamako ba.
“Wasu sai su shafe kwanaki da yawa, ba a ma sake dibar gwajin na su ba, ballantana a kawo musu sakamako.” Cewar sa.
An tuntubi Shugaban Kwamitun Likitocin Yaki Da Coronavirus na Kano, Tijjani Hasan, ya ce ba shi da labarin hakan ya afku.
Discussion about this post