Manajan Otel din da Wike ya rusa a Ribas ya kamu da cutar Korona

0

Bayanai sun nuna cewa manajan Otel din Prodest Hotel Eleme na daya daga cikin mutanen da suka kamu da cutar Covid-19 a cikin kwanakin nan a jihar Ribas.

Otel din Prodest Hotel, Eleme na daya daga cikin Otel-Otel din da gwamnan jihar Ribas Wike ya bada umurnin a rusa domin yin taurin Kai ga dokar hana yada cutar Korona da gwamnati ta saka a jihar.

Kwamishinan yada labarai Paulinus Nsirim ya Sanar da haka wa manema labarai a jihar.

” Hakan ya tabbatar da hukuncin rusa Otel din da aka yi bayan kin bin umarnin dokar hana yada cutar Korona a jihar da aka saka.

Bisa ga sakamakon gwajin da Hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa jihar ta samu karin mutum 27 da suka kamu da cutar.

Tsakanin ranar 13 zuwa 20 ga watan Mayu jihar ta samu akalla mutum 52 da suka kamu da cutar.

A yanzu haka adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a jihar sun kai 116 an kuma sallami 30 daga cikin su, 78 na kwance a asibiti har yanzu, 8 sun mutu.

Yanzu sama da mutum 8000 suka kamu da cutar a Najeriya, sama da mutum 2000 sun warke, akalla mutum sama da 200 sun rasu.

Domin dakile yaduwar cutar gwamnati jihar ta dauki wasu tsauraran makatakai da Za su taimaka wajen kare kiwon lafiya mutane a jihar.

Share.

game da Author