Majalisar Zartaswa ta amince wa Ministan Gona ciwo bashin kayan noma na dala bilyan 1.2

0

Majalisar Zartaswa ta amimce a ciwo bashin dala bilyan 1.2 domin wadata harkar noma da manoma da kayan aikin gona.

Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa da aka yi ranar Laraba tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan taro da aka gudanar ta tsarin talbijin ta kai-tsaye, yayin da kowane Minista ke halartar taron daga ofishin sa, amma kowa ba kallon juna, Hukumar Dakile Cututtuka Maso Yaduwa (NCDC) ce ta bada shawarar gudanar da shi ba tare da Ministocin sun hadu wuri daya ba, saboda tsoron kamuwa da cutar Coronavirus.

Nanono bai yi karin haske ba dangane da yadda za a ciwo bashin ba. Amma dai kwanan nan Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta fi maida hankali ne ga ciwo bashi a cikin gida, maimakon a rika dogaro da kasashen waje, saboda barnar da Coronavirus ta yi wa duniya.

Nanono ya bayyana cewa kananan hukumomi 632 ne za su ci moriyar bashin.

Minista Nanono ya kara da cewa, “a yau Ma’aikatar Gona da ta Harkokin Kudade sun mika roko domin a amince a ciwo bashin dala bilyan 1.2.

“Wadannan an yi haka domin kananan hukumomi 632 da kuma kananan masana’antun harkokin noma su samu bunkasa da kayan noma.

“Wannan zai kasance wani sauyin da zai zama gagarimin shirin da ba a taba ganin kamar sa ba.

A nasa bangaren, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, ya ce an amince a sai wa Hukumar Kula da Tashoshin Giragen Ruwa bashin za ta ciwo bashin naira milyan 683 wadanda za a sayo wa manyan hukumar kartsa-kartsan motoci guda 19.

“Wannan ne karo na farko da Hukumar NPA za ta yi motoci a cikin shekaru hudu cur. Shi ya sa aka amince ba tare da wani ka-ce-na-ce ba.

“Ba motocin alfarma na shiga ba ne. Dukkan su samfurin Toyota Hilux ne domin karakainar aiki.

Nanono ya ce za a yi amfani da kidaden ramcen wajen sauyen taraktocin noma a cibiyoyin kananan hukumomi 632.

Ya ce za a kafa cibiyoyin gyaran tarakta wadanda za su rika aikin noma ana biyan su.

Ya ce duk wanda aka bai wa bashin tarakta ga manoma su biya cikin shekaru hudu. Daga nan tarakta ta zama ta su kenan.

Share.

game da Author