MACE-MACE: Jarman Kano Isa Hashim ya rasu kwana daya bayan mutuwar Sarkin Rano

0

Jarman Kano, kuma daya daga cikin manyan mashahuran dattawan Kano da suka rage, Farfesa Isa Hashim ya rasu.

Hashim ya rasu ya na da shekaru 86 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya ta wani takaitaccen lokaci.

Ya rasu ranar Lahadi da safe, kwana daya bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Rano, Tafida Abubakar, wanda PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin rasuwar sa ranar Asabar.

Daya daga cikin ‘ya’yan sa mai suna Dija Hashim, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahaifin na su bai wani dade ya na wani ciwon da ya kwantar da shi ba.

Sai dai kuma wani a cikin iyalan mamacin ya bayyana wa wakilin mu cewa ya rasu ne sakamakon damuwar mutuwar wasu manyan abokan sa da suka tashi tare, wanda suka rika mutuwa bi-da-bi, kwanan nan a Kano.

Wannan rasuwa da ta Sarkin Rano, ta zo ne a daidai lokacin da Shugaban Tawagar Shugaban Kasa kan dakile Coronavirus a Kano, Nasiru Gwarzo ya shaida wa BBC Hausa cewa mace-macen da ake fama da su a Kano na da alaka da cutar.

Hashim wanda tsohon farfesa ne, ya yi aikin gwamnati zuwa matakin Babban Sakatare. Ya yi ritaya ya koma ya na koyarwa tsawon shekaru da dama a Jami’ar Bayero, Kano.

Ya rasu bayan rasuwar Farfesa Ayagi, Dakta Muhammad Uba Adamu, Farfesa Balarabe Maikaba da wasu farfesoshin uku duk a Kano.

Share.

game da Author