Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa likitoci 8 sun kamu da cutar Korona a jihar Zamfara.
Mataimakin Shugaban Kungiyar reshen jihar Zamfara Mannir Bature ya Sanar da haka wa manema labarai a jihar yana mai cewa adadin yawan likitocin da suka kamu da cutar sun kai kashi 10 na yawan mutanen dake dauke da cutar a jihar.
Bayyanai sun nuna cewa likitoci sun kamu da cutar ne a jikin marasa lafiyan dake dauke da cutar ba tare da sun sani ba.
Bature ya ce kashi 60 na likitocin da suka kamu da cutar sun warke saura na samun sauki a asibitocin da suke kwance. Sannan kuma wasu likitoci 30 sun killace kan su a dalilin gwamatsuwa da suka yi da likitocin da suka kamu.
Gano cutar a jikin likitoci ya tada wa likitoci sama da 300 hankali a jihar inda hakan ke kawo koma baya a aikin su.
Bature ya yi kira ga gwamnati da ta horas da dalibai likitoci domin kara yawan likitocin da za su rika aikin kula da masu fama da cutar da cutar Korona a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar 7 ga watan Mayu Kungiyar Nas-nas da Unguwar Zoma ta Kano ta ce jami’an ta 18 sun kamu da cutar.
Kungiyar Likitocin NMA reshen jihar Kano ta ce Likitoci 34 ne suka kamu da cutar a Kano.