Likitoci 34 sun kamu da Coronavirus, daya ya mutu a jihar Kano

0

Kungiyar likitoci Najeriya (NMA) rashin jihar Kano ta sanar cewa akalla likitoci 34 ne suka kamu da cutar Coronovirus, daya ya mutu daga cikin su a jihar Kano.

Shugaban Kungiyar Sanusi Bala ya fadi haka da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano ranar Talata.

Bala ya ce mafi yawan likitocin da suka kamu da cutar na aiki da asibitin Aminu Kano sauran kuwa na aiki ne da asibiti masu zaman kansu a jihar.

Ya ce likitocin sun kamu da cutar ne yayin da suke kula da mutanen da ake zargin sun kamu da cutar.

Bala ya ce Kungiyar za ta ci gaba da samar wa likitoci kariya a wajen aikin kula da marasa lafiya.

Bayan haka shugaban asibitin Aminu Kano Hauwa Muhammed ta sanar cewa tuni asibitin ta samar da isassun kayan samar da kariya daga kamuwa da cutar ga likitocin da suke aiki a Asibitin.

Hauwa ta ce sun raba kayan wa duk ma’aikatan kiwon lafiya da kuma tare da horas da su sanin mahimmancin amfani da kayan.

Jihar kano ce jiha ta biyu da tafi yawan wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya baya ga jihar Legas.

Sannan kuma Almajirai da dama da aka maida su wasu jihohin kasar nan sun kamu da cutar inda kamar a jihar Kaduna, ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce samam da Almajirai 50 da aka dawo dasu jihar daga Kano duk sun Kamu da cutar.

Share.

game da Author