Kwankwaso ya nemi SSS da Gwamnatin Kaduna su fito da Dadiyata

0

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya yi kira ga jami’an SSS da Gwamnatin Jihar Kaduna su saki wani mai goyon bayan tafiyar akidar siyasar sa ta Kwankwasiyya, Abubakar Idris da aka fi sani da suna Dadiyata.

Cikin dare ne a ranar 2 Ga Agusta, 2019 wasu da ba a san ko su wa ne ba, su ka same shi har gidan sa a Kaduna suka yi aqon gaba da shi, kuma har yau babu labari.

Dadiyata dan shekaru 34, ya na koyarwa ne a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma, Jihar Kaduna.

Ya kasance mai goyon bayan Kwankwaso, kuma mai sukar Gwamnatin Kano karkashin Abdullahi Ganduje da Gwamnatin Kaduna.

A baya, ya kasance mai sukar Gwamnatin Goodluck Jonathan, a gefe daya kuma ya na goyon bayan Buhari.

Bayan an kafa mulki, Dadiyata ya bi tafiyar Kwankwasiyya, ya rika sukar Gwamnatin Buhari da ta Ganduje.

Bayan an yi dukkan kokarin gano shi abu ya ci tura, masu adawa sun rika zargin cewa ‘yqn siyasar da ya ke adawa da su ne musabbabin bacewar ta sa, ko suka batar da shi.

Iyalan Dadiyata sun maka SSS, Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna da Gwamnatin Kaduna kara cewa au fito musu da Dadiyata.

Yan sanda sun sha nanata cewa sun yi duk iyakar kokarin nemo duk inda ya ke, amma abu ya ci tura.

Sai dai kuma Kwankwaso a baya ya sha suka, ganin yadda ya yi shiru ba a jin ya na babatun neman inda Dadiyata ya ke

Sai dai kuma a wata hira ta bidiyon Instagram da ya yi da mawallafin Ovation, Dele Momudu, Kwankwaso ya ce kasa gano Dadiyata da jami’an tsaro suka yi, abin damuwa ne matuka.

Ya bayyana Idris Dadiyata a matsayin hazikin mutum kuma nagari.

“Akwai wani mai goyon bayan tafiyar mu kuma jajirtaccen malamin Jami’ar Gwamnatin Tarayya da
aka je aka kama har gidan sa a Kaduna a gaban iyalan sa, cikin shekarar da ta gaba ta, amma har yau babu labarin halin da ya ke ciki.” Inji Kwankwaso.

“Mun yi ta kokarin mu ta hannun SSS domin ganin an gano inda ya ke, amma abin ya ci tura. Don haka ina kira ga gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin tarayya da duk wani da harkar tsaro ke hannun sa su maida wannan mutumi gida a cikin iyalan sa.”

Share.

game da Author