KUDIRIN DOKAR CUTUTTUKA: Bill Gates ya karyata yarfen bai wa Majalisar Tarayya cin hancin dala milyan 10

0

Hamshakin attajirin nan na duniya, mai Microsoft, Bill Gates, ya karyata abin da ya kira yarfe da karairayin da aka rika watsawa cewa ya bai wa Majalisar Tarayyar Najeriya toshiyar-bakin dala milyan 10 domin su gaggauta sa wa Kudurin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa hannu.

Ranar Litinin ce Jami’in Gidauniyar Bill & Melinda da ke Najeriya, Paulin Basinga ta karyata wannan zargi a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin majalisa, domin zuwa musamman ta karyata zargin.

Wannan zargi ya fito ne daga wata kungiyar rajin kare hakkin jama’a, mai suna CUPP, a daidai lokacin da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya rika hakikicewa lallai sai a gaggauta amincewa da kudirin, duk kuwa da cewa mafi yawan ‘yan majalisar ba su mallaki kudin kudirin mai babi 82 ba, ballantana su samu damar karanta shi su kuma fahimci abin da ya kunsa.

Yayin da ake cikin wannan dambarwa a kan kudirin wanda Kakakin Majalisa din ne ya gabatar da shi, zai kungiyar CUPP ta fitar da sanarwa, ta bakin shugaban ta Imo Ugochinyere cewa, wasu bayanai sun fado hannun ta da ke nuna cewa Bill Gates ne ya bada toshiyar baki domin a gaggauta amincewa da kudirin.

Sai dai kuma Basinga ta ce Gidauniyar Bill & Melinda ba ta yi wannan bayar da kudin ba, kuma ba za ta taba tsoma kan ta cikin wata harkalla mai kama da wannan, koma wata iri daban ba, a dukkan kasashen da gidauniyar ke aikin tallafin jinkai.

Ta ce karya ce kawai da yarfe da sharrin bata suna kawai.

Yayin da Majalisar Tarayya ta yi kurarin kai wanda ya yi wannan ikirari kotu, Kungiyar Gwamnonin Arewa ita ma ta nuna rashin amincewar ta da Kudirin.

Wasikar da Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya aika wa Majalisar Tarayya a madadin gwamnonin Najeriya 36, ta bata wa shugabannin majalisar rai, har suka maida masa zazzafan martani.

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin dambarwar Gwamnonin da Shugabannin Majalisar Tarayya da kuma bayanin abin da kudirin dokar ya kunsa.

Rahoton na makon jiya ya bayyana yadda Majalisar Tarayya ta maida wa Tambuwal da Gwamnonin Najeriya raddi.

Majalisar Tarayya ta maida wa Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto kakkausan raddi, dangane da matsayar da Gwamnonin Najeriya suka dauka, cewa a jingine Kudirin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a cikin jama’a, bisa dalilin cewa Majalisar Tarayya ba ta tuntubi gwamnonin ba.

Kudirin dokar dai Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya kirkiro shi.

Cikin wata takardar kakkausan raddi da Majalisa ta maida Tambuwal, wanda ya sa wa takardar gwamnoni hannu, a madadin sauran gwamnonin, Kakakin Yada Labaran Majalisa, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa bai ga dalilin shisshigin gwamnoni na rubuto takardar ba, domin tuni majalisa ta jingine kudirin, ta ce za a ji ra’ayoyin jama’a tukunna.

Tambuwal Nukura Ya Ke Wa Gbajabiamila -Ben Kalu

Benjamin Kalu ya ce ba wani abu ya sa Gwamna Tambuwal ke ta sagarabtu a kan kudirin ba, sai nukura kadai da ya ke wa Shugabancin Majalisar Tarayya, a karkashin Femi Gbajabiamila.

Kalu ya kara da cewa Tambuwal ya lura Majalisa a yanzu sai kara samun tagomashi ta ke yi, sabanin lokacin da ya yi shugabancin ta, da kuma bayan saukar sa, tsakanin 2015 zuwa 2019.

“Tambuwal ya sani sarai a matsayin sa na gogaggen tsohon dan majalisar tarayya, wanda har shugabancin majalisa ya rike, kudiri iri-iri ne.

“Akwai kudirin da ba ya bukatar sai an kai wa Majalisar Dokokin Jihohi ko Gwamnoni kafin a amince da shi ya zama doka.

A Cire Tambuwal Daga Cikin Kwamitin Tattaunawa Da Majalisa

“Mun Amince cewa gwamnoni abokan tafiyar Majalisar Tarayya ne wajen ciyar da kasar nan gaba. To amma fa ya kamata su sani cewa mu ba ‘yan-amshin-Shatan su ba ne, kuma ba a karkashin gwamnoni mu ke ba. Sai fa idan a yanzu so su ke yi a sauya doka mu koma karkashin su.

“Ba mu yadda da Gwamna Tambuwal a cikin sunayen gwamnoni uku da za su yi zaman tattaunawa da shugabannin majalisa ba. Domin tuni ya nuna son rai a cikin lamarin. Kasancewar sa tsohon Shugaban Majalisar Tayyaya, zai iya yin kane-kane, ya hana sauran bakin magana.”

Waiwaye: Yadda Tambuwal Ya Fusata Shugabannin Majalisar Tarayya

Ranar Alhamis PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin taron-dangin da daukacin Gwamnonin Najeriya 36, su ka yi wa Majalisar Tarayya, inda su ka ce sun ki amincewa da Kudirin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa, wadda yanzu haka ake tafka kwatagwangwamar hayaniya saboda ita a Majalisar Tarayya.

Kudirin dokar mai suna ‘Control of Infectious Diseases Bill’, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi a Majalisa.

Duk da cewa bai samu na’am da karbuwa daga masu yawan mambobin majalisar ba, tuni kudorin har an yi masa karatu na biyu a zauren majalisa, kafin korafe-korafe, suka, caccaka su sa a dakatar da batun sa.

Yadda Kudirin Dokar Ya Yi Bakin Jini

Kafin Gwamnonin Najeriya su nuna rashin amincewa da kudirin, ‘yan Najeriya da dama da wasu ‘yan Majalisa duk sun nuna damuwa dangane da yadda ake ta gaggawa, azarbabi da rawar jikin hanzarta amincewa da kudirin.

Ana ta mamakin yadda a ranar da aka gabatar da kudirin yadda Shugaban Majalisa, Femi Gbajabiamila ya hakikice wajen amimcewa da kudirin, duk kuwa da cewa kusan gaba dayan ‘yan majalisar ko samun damar lokacin karanta kudirin mai babi 82 ba su yi ba.

Wannan kurman karatu da Gbajabiamila ya biya wa mambobi, ya haifar da rashin amimcewa daga ‘yan Najeriya masu bibiyar al’amurran yau da kullum.

Kudiri Ko Satar-fasaha?

An rika yin tir da cewa gaba dayan kudirin wankiya aka yi daga wata dokar kasar Singapore, wadda kasar ke amfani da ita wajen kokarin dalile cututtuka masu yaduwa.

Salon rubutu, Turancin da aka yi amfani da shi da kalmomin da ke cikin kudirin mai babi 82, an tabbatar da cewa duk satar-fasaha ce aka kwafo daga dokar Singapore.

Kungiyoyin kare hakkin jama’a kuma sun rika yin kururuwar cewa kudirin idan ya zama doka, to za ta takura kuma ta danne hakki tare da tirsasa wa ‘yan Najeriya yin abin da bai dace a tirsasi a karkashin mulkin dimokradiyya ba.

An kuma yi korafi a kan wani babi, wanda zai tilasta kowane mai fita kasashen waje da mai shigowa sai ya mallaki katin shaidar lafiyar sa garau. Wannan wani kati daban aka bijiro da shi a cikin kudirin, wanda ba ‘yelo card’ da matafiya suka sani ana amfani da shi ba.

Ba Mu Yarda Da Kudirin Ya Zama Doka Ba -Gwamnonin Najeriya

Cikin takardar da Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal, Gwamnan Sokoto ya sa wa hannu, gwamonin su 36, sun ce sun ki amincewa da kudirin domin ba a tuntube su ba, a matsayin su na jagororin jama’ar da ake kokarin a kakaba wa dokar.

Sun kara da cewa ya kamata a nemi jin ra’ayin jama’a kafin a yi azarbabin yanke hukuncin neman a mayar da kudirin zuwa doka.

Sannan kuma Gwamnonin sun karta alamar tambaya dangane da karfin ikon tirsasa killace mutum da kuma tilasta yi masa allurar rigakafi da kudirin dokar ya bai wa Ministan Lafiya da Shugaban Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).

Gwamnonin sun ce tilas majalisa ta jingine kudirin. Sannan kuma sun nada gwamnonin Sokoto, Katsina da Filato su zauna su yi nazarin kudirin daga nan su zauna da shugabannin Majalisar Tarayya domin a sake tsefe gashin kan kudirin dokar gaba daya, ba don komai ba, suka ce don kada a yi wa ‘yan Najeriya kitso da kwarkwata.

Share.

game da Author