Jihar Taraba ta ki amincewa ta karbi lodin wasu almajirai ‘yan asalin jihar da jihar Nasarawa ta kwaso, ta nemi jibge ma ta su a ranar Talata.
Tun a ranar Lahadi ne aka isa Jalingo, babban birnin Jihar Taraba dauke da lodin almajiran masu dimbin yawa, wadanda ke a karkashin rakiyar jami’an Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Nasarawa.
Jihar Taraba ta ki ba su makwanci, wanda hakan ya sa sai dai suka kwana a wajen kofar ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha. Ba a saurare su ba, sai karfe 10 na safe.
‘Ku Fita Wajen Gari Ku Jira Tukunna’
An umarci almajiran su koma can wajen garin Jalingo su zauna daidai jikin wani allon ‘sambodi’ wanda ke dauke da kalmomin yi wa matafiya maraba da shigowa Jalingo.
Wannan allo dai ya na kan hanyar shiga Jalingo daga garin Wukari.
Majiya ta ce sai can wajen karfe 12:45 na rana jami’an gwamnati daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, suka dunguma suka isa wurin da aka saukar da dandazon almajiran.
Sun je masu ne da takarda rubutacciya daga Sakataren Gwamnatin Taraba zuwa ga Sakataren Gwamnatin Nasarawa, inda aka shaida masa kin karbar almajiran. Kuma aka ce jami’an da suka kai su Taraba, su kwashe su su koma inda suka fito.
Babban Sakatare na Ofishin Sakataren Gwamnati, Sudday Maiyaki ne ya sa hannu a kan takardar, a ranar 4 Ga Mayu, 2020.
Abinda wasikar Taraba ta kunsa zuwa ga Nasarawa
“Mum kasa tantance hakikanin yawan almajiran da ku ka lodo zuwa Taraba. Kunce su 102, amma dai mu guda 79 ne suka iso mana.
Jihar Taraba ta yanke shawarar maido muku wadannan almajirai, sai kun tantance Karamar Hukumar da kowanen su ya ke a Taraba. Sannan kuma sai kun bada shaidar kowanen su ba shi dauke da cutar Coronavirus.
“Idan za a sake dawo da su Jihar Taraba, to a dunguma a taho har da malaman su, saboda su za a tasa a gaba su a kai kowane yaro a gaban iyayen sa.”
Taraba Ta wulakanta mu -Jami’in Nasarawa
Wani daga cikin jami’an Nasarawa ya bata rai matuka ganin yada Taraba ta ki yi musu shimfidar fuska, ballantana shimfidar tabarma.
Ya ce bayan an tara almajiran, sai da aka killace su a cikin gininwata makarantar sakandare, kuma aka yi musu gwaji, duk aka tabbatar cewa na su dauke da cutar Coronavirus.
Ya kuma nuna takaicin yadda aka bar su waje suka kwana cikin motoci. Sannan ya ce an ba su tukuicin naira 100,000 aka ce su zuba mai su koma Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa.
Sama da almajirai 1,000 nr aka tara a jihar Nasaraw, a kokarin da jihar ke yi ba maida kowane almajiri garin su wajen iyauen sa.
Discussion about this post