Kowa ya yi Sallar Idi a cikin gidan sa -Sultan, JNI

0

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, sun umarci daukacin Musulmin Najeriya kowa ya gudanar da Sallar Idi a gida, gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Cikin wata sanarwar da JNI ta fitar ta hannun Babban Sakatare Khalid Aliyu, ya ce tunda an hana cunkoson jama’a cikin har da gwamutsuwar jama’a a wuraren ibada, ya kamata Musulmi su bi wannan umarni, domin kawar da wannan cuta ta Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta umarci a fara duban watan 1 Ga Shawwal a ranar Juma’a kafin Sallar Magriba da kuma bayan Magriba.

Cikin sanarwar da JNI ta fitar, ta ce kowa ya yi Sallar Idi a cikin gida tare da iyalin sa, idan kuma shi kadai ne ya kama zai yi sallar sa.

Yadda Ake Sallar Idi A Cikin Gida -JNI

Karamar Sallah:

1. Ba a yin huduba, kuma takaitawa ake yi.

2. Raka’ar Farko za a yi kabbara 7, sannan a karanta Fatiha da Suratul A’ala, ko kuma surar da mutum zai iya.

3. Raka’a ta Biyu za a yi kabbara 7, a karanta Fatiha da Suratul Ghashiyah.

Karin bayani: Hadisan Anas bin Malik da wasu hadisai ne suka ruwaito haka.

JNI ta yi karin bayanin cewa a jihohin da Gwamnonin su suka amince a yi Sallar Idi, to a yi kaffa-kaffa, kowa ya sa takunkumin hanci da baki, kuma kada a gwamutsu.

JNI ta yi fatan Allah ya maimaita, ya bada ladar azumin watan Ramadan.

Share.

game da Author