Kotun Koli ta sallami Uzor Kalu daga kurkuku, ta ce a sake shari’ar

0

A ranar Juma’a ce Kotun Koli ta sallami tsohon Gwamnan Jihar Abia, Uzor Kalu daga kurkuku, kuma ta umarci a sake shari’ar sa a Babbar Kotun Tarayya.

Alkalin Kotun Koli, Mai Shari’a Ejembi Eko, ya ce an tabka kwamacala wajen daurin da Mai Shari’a Mohammed Idris ya yi wa Kalu a Babbar Kotun Tarayya, Lagos.

Eko ya ce lokacin da Idris ya daure Uzor Kalu, an rigaya an kara masa mukami zuwa Kotun Daukaka Kasa ta Kasa.

“Don haka babu yadda za a yi kuwa mai shari’a a Kotun Daukaka Kara ya yanke hukunci a Kotun Koli.” Inji Eko, a lokacin da ya ke yanke hukumcin sallamar Kalu daga zaman watanni shida da ya yi a kurkuku.

Sai dai kuma Eko umarni ya bayar ga Shugaban Alkalan Banbar Kotun Tarayya ya sa wani Alkalin Babbar Kotun Tarayya ya sake shari’ar Kalu tare da ta Ude Udeogu da aka daure su tare.

Udeogu shi ne Daraktan Harkokin Kudade na Gidan Gwamnatin Abia, a lokacin da Kalu ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2007.

An daure Kalu cikin Disamba bayan an same shi da laifin wawurar naira bilyan 7.65 a asusun Gwamnatin Jihar Abia, a lokacin da ya ke gwamna.

Share.

game da Author