KORONA: Najeriya ta zarce mutum 9000, mutum 2,697 sun warke

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 387 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 254, FCT – 29, Jigawa – 24, Edo – 22, Oyo 15, Rivers – 14, Kaduna 11, Borno – 6, Kano – 3, Plateau – 2, Yobe – 2, Gombe – 2, Bauchi – 2, and Ondo – 1.

Yanzu mutum 9,302 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 6334 na dauke da cutar, mutum 2,697 sun warke, 261 sun mutu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Ga yawan adadin wadanda suka kamu cutar a Najeriya a jihohi.

Lagos 4,337, Lagos – 942, FCT – 564, Katsina – 358, Borno – 264, Oyo – 275, Ogun – 246, Jigawa – 265, Edo – 262, Bauchi – 236, Kaduna – 232, Rivers – 190, Gombe – 156, Sokoto – 116, Plateau – 101, Kwara – 86, Zamfara – 76, Nasarawa – 62, Delta – 57, Yobe – 49, Osun – 44, Adamawa – 38, Ebonyi – 40, Akwa Ibom – 45, Imo – 34, Kebbi – 33, Niger – 30, Ondo – 25, Ekiti – 20, Enugu – 18, Taraba – 18, Bayelsa – 12, Anambra – 11, Abia – 10, Benue – 7 and Kogi – 2.

Share.

game da Author