Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 216 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Lilini.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Litini, Jihar Legas ta samu karin mutum 74,33-Katsina, 19-Oyo, 17-Kano, 13-Edo, 10-Zamfara, 8-Ogun
8-Gombe, 8-Borno, 7-Bauchi, 7-Kwara, 4-FCT, 3-Kaduna, 3-Enugu, 2-Rivers.
Yanzu mutum 6175 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1644 sun warke, 191 sun mutu.
Idan ba a manta ba shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da tswaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.
Discussion about this post