Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 307 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 188, FCT – 44, Ogun – 19, Kaduna – 14, Oyo – 12, Bayelsa – 9, Gombe – 5, Kano – 3, Delta – 3, Imo – 2, Rivers – 2, Niger – 2, Bauchi – 2, Plateau – 1 and Kwara – 1.
Yanzu mutum 10,162 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3007 sun warke, 287 sun mutu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.
A ranar Lahadi kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da sama da 188. Akalla jihohi 15 sun samu karin mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 4943, sai jihar Kano – 954, FCT – 660, Katsina – 364, Edo – 284, Oyo – 292, Borno – 271,Jigawa – 270, Ogun – 278, Kaduna – 258, Bauchi – 238, Rivers – 206, Gombe – 161, Sokoto – 116, Plateau – 105, Kwara – 88, Delta – 83, Zamfara – 76, Nasarawa – 62, Yobe – 52, Akwa Ibom – 45, Osun – 45, Ebonyi – 40, Adamawa – 38, Imo – 36, Kebbi – 33, Niger – 32, Ondo – 25, Ekiti – 20, Enugu – 18, Taraba – 18, Bayelsa – 12, Anambra – 11, Abia – 10, Benue – 7 and Kogi – 2.