Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 265 da suka kamu sannan mutum 10 sun mutu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Juma’a.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Juma’a, Jihar Legas ta samu karin mutum 133, 34-Oyo, 28-Edo, 23-Ogun, 22-FCT, 6-Plateau, 5-Kaduna
3-Borno, 3-Niger, 2-Kwara, 2-Bauchi, 2-Anambra, 2-Enugu
Yanzu mutum 7526 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2174 sun warke, 221 sun mutu.
Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa akwai yiwuwar za a fara sallaman wadanda suka kamu da Korona da suka fara jin sauki daga asibitocin kasar nan.
Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 a Abuja.
Ya ce gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne bisa ga sakamakon binciken da aka gabatar game da cutar dake nuna cewa za a iya sallaman wanda ke dauke da cutar daga asibiti idan ya fara jin sauki a jikinsa. Zai koma gida ya killace kan sa ma’aikata na zuwa suna duba shi suna bashi magani.
” Muna duba yiwuwar wannan abu har yanzu domin ganin ko za a yi aiki da shirin a kasar nan. Sannan muna wayar wa mutane kai game da haka saboda gujewa korafe-korafen da za su yi idan gwamnati ta amince a rika haka.
Karancin gadajen kwantar da marasa lafiya a kasar nan.
Bayanai sun nuna cewa gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne saboda karancin gadajen kwantar da masu fama da cutar a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa jihar Legas, Kano da Abuja na cikin wurarren dake fama da karancin gidaje a kasar nan kuma sune suka yawan masu dauke da cutar.
Ihekweazu ya ce gwamnati na yin nazarin yadda za a kima ana kula da mutane a gidajen su ne maimakon idan sun kamu a dauko subzuwa asibiti saboda karancin gadajen asibiti.
“A duk fadin kasar nan gadajen kwantar da masu fama da coronavirus guda 3,500 ne muke da su sannan a yanzu haka asibitocin killace masu fama da cutar na gab da cika a jihar Legas.
Yanzu mutum 7016 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1907 sun warke, 211 sun mutu.
Yi wa mutanen da suka warke gwajin cutar sau daya a maimakon biyu.
Ihekweazu ya ce nan gaba za a fara yi wa wadanda suka warke gwajin cutar sau daya ne maimakon sau biyu da aka saba yi.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta fahimci cewa duk wanda ya warke kuma aka yi masa gwaji na farko sakamakon na nuna baya dauke da cutar ko da an sake yi masa gwaji na biyu.
Ya ce da a zauna ana yi wa mutumin da ya warke gwaji sai biyu gwara a yi gwajin sau daya a sallame shi kawai.
Ihekweazu ya ce yin haka zai rage yawan cinkoson mutane sannan da karancin gadajen da ake fama da su a asibitocin kasar nan.
SHARE.