Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 226 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Talata.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Talata, Jihar Legas ta samu karin mutum 131, 25-Ogun, 15-Plateau, 11-Edo, 7-Kaduna, 6-Oyo, 5-FCT
5-Adamawa, 4-Jigawa, 4-Ebonyi, 4-Borno, 3-Nasarawa, 2-Bauchi, 2-Gombe, 1-Enugu, 1-Bayelsa.
Yanzu mutum 6401 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1734 sun warke, 192 sun mutu.
Idan ba a manta ba shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da tswaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.