Gwamnati jihar Jigawa ta bayyana cewa cutar coronavirus ta kashe mutum hudu a jihar da hakan ya kawo adadin yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar zuwa 7 a jihar.
Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar Abba Zakari ya ce an kuma sallami mutum 32 daga asibitin kula da masu fama da cutar.
A yanzu haka mutum 143 ne aka sallama a jihar.
“Daga cikin mutum 7 din da suka mutu a jihar uku sun mutu a asibiti, hudu sun a gidajen su.
“Bincike ya nuna cewa mutum hudu din da suka mutu a gida sun fito daga gararuwar Ringim, Birnin-Kudu da Gwaram ne.
Zakari ya ce ma’aikatan kiwon lafiya sun fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka kamu da cutar a dalilin yin cudanya da mutum hudu din da suka mutu a gida.
Idan ba a manta ba a ranar Litini Hukumar NCDC ta Sanar cewa an samu karin mutum bakwai da suka rasu a Najeriya inda Zakari ya ce mutum hudu daga ciki daga jihar Jigawa suke.
Jihar ta kuma fara sallman mutanen da suka warke bayan an yi musu gwajin cutar sau daya.
Yin haka zai taimaka wajen rage cunkoson mutane a asibitocin kula da masu fama da cutar a jihar.
Bayan haka Zakari ya ce mai taimakawa gwamnan jihar Muhammad Badaru kan harkokin yaki da jahici Ibrahim Isma’il na daga cikin mutum hudu din da suka mutu a jihar.
Ibrahim Isma’il ya rasu a asibitin kula da masu fama da cutar Covid-19 Bayan ya fara nuna alamun kamuwa da cutar.
Kafin ya rasu Isma’il ya rike sarautar Jarman Ringim na masarautar Ringim a jihar.
Gwamnan Badaru ya aika da wasikar ta’aziya ga mutane da masarautar Ringim inda yake cewa Isma’il mutumin kirin ne da dattaku.