KORONA: Kano ta bude sabbin wuraren dibar jini 9

0

Shugaban kwamitin dakile yaduwar Coronavirus na jihar Kano Tijjani Hussaini ya ce gwamnatin Kano ta kafa sabbin wuraren gwajin Samfari 9 a fadin jihar.

Tijjani ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya cewa an kafa wurare 8 a cikin garin Kano, daya a karamar Hukumar Rano.

Bayan haka Tijjani ya Kara da cewa Gwamnati za ta kafa iren-iren wadannan wurare a duka kananan hukumomin jihar.

” Zuwa yanzu cutar ta yadu a kananan hukumomin 31 cikin 44 sake jihar Kano.

Mutum 923 ne suka kamu da cutar a jihar, an sallami mutum 134, 38 kuma sun riga mu gidan gaskiya.

Idan ba a manta ba Ma’aiktan jihar Kano sun bayyana rashin jin dadin su tun daga ranar Alhamis din makon jiya da gwamnati ta biya su albashin watan Mayu.

Da yawa da suka zanta da PREMIUM TIMES sun shaida cewa gwamnati bata kyauta musu ba zaftare musu albashi da tayi.

” Ni dai kusan naira 20,000 aka cire min a albashina. Gaba daya ya dagula min lissafin da nayi na shirin Sallah. Wannan abu bai yiba.” Inji ma’aikaci

Ma’aikata sun ce gwamnati ta yanke musu albashi ba tare da sanar dasu su kwana da shiri ba. ” Kawai sai ka je cire kudi sai ATM ta yi maka kararrawa, cewa kudin ka bai kai ba.

Wasu sun ce gwamnati ya yanke karin da tayi wa ma’aikata ne da ta daga karancin Albashi daga 18,000 zuwa 30,000 sai ta maida albashir yadda yake ada.

Share.

game da Author