Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 146 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Talata.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Talata, Jihar Legas ta samu karin mutum 57, 27-Kano, 10-Kwara, 9-Edo, 8-Bauchi, 7-Yobe, 4-Kebbi, 4-Oyo
3-Katsina, 3-Niger, 2-Plateau, 2-Borno, 2-Sokoto, 2-Benue, 1-Gombe, 1-Enugu, 1-Ebonyi, 1-Ogun, 1-FCT, 1-Rivers.
Yanzu mutum 4787 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 959 sun warke, 158 sun mutu.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar Covid-19 da aka sallama a jihar sun kai 502 a jihar.
Ma’aikatar ta ce an sallami mutum 33 da suka warke daga cutar a jihar ranar Litini.
A lissafe dai adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar sun kai kwatan mutanen da suka kamu da cutar kuma ke kwance a asibiti a jihar.
Ma’aikatar ta ce mata 9 da maza 24 na daga cikin mutanen da aka sallama daga asibitocin kula da masu fama da cutar coronavirus dake Onikan da Eti-Osa.
Mutum 1,861 ne suka kamu da cutar a jihar.
Daga ciki 1,308 na kwance a asibiti, an sallami 502, 33 sun mutu.
Kwamishinan Jihar Legas, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu dauke da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Legas, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.
Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.