KORONA: Jigawa 23, Bauchi 16, Katsina 16, Abuja 10, Yanzu mutum 4971 suka kamu a Najeriya, 164 sun rasu

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 184 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Laraba.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Laraba, Jihar Legas ta samu karin mutum 51, 23-Jigawa, 16-Bauchi, 16-Katsina, 14-Kano, 10-FCT, 10-Rivers, 9-Kwara, 5-Delta, 5-Kaduna, 4-Sokoto, 4-Oyo, 3-Kebbi, 3-Nasarawa, 3-Osun, 2-Ondo, 1-Ebonyi, 1-Edo, 1-Enugu, 1-Anambra, 1-Plateau
1-Niger.

Yanzu mutum 4971 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1070 sun warke, 164 sun mutu.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar Covid-19 da aka sallama a jihar sun kai 502 a jihar.

Ma’aikatar ta ce an sallami mutum 33 da suka warke daga cutar a jihar ranar Litini.

A lissafe dai adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar sun kai kwatan mutanen da suka kamu da cutar kuma ke kwance a asibiti a jihar.

Ma’aikatar ta ce mata 9 da maza 24 na daga cikin mutanen da aka sallama daga asibitocin kula da masu fama da cutar coronavirus dake Onikan da Eti-Osa.

Mutum 1,861 ne suka kamu da cutar a jihar.

Daga ciki 1,308 na kwance a asibiti, an sallami 502, 33 sun mutu.

Kwamishinan Jihar Legas, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu dauke da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Legas, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.

Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.

Share.

game da Author