Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kano ta bayyana cewa an samu karin mutum shida da suka rasu a dalilin fama da suka yi da cutar Korona.
Ma’aikatar ta sanar cewa baya ga mutum shida da suka rasu, mutum 63 sun warke daga cutar ciki harda Kabiru Rabiu, wadda shine mutumin da ya shigo Kano da cutar ya rike boye-boye ya ki fadi wa likitoci gaskiyar abinda ke damun sa.
Idan ba a manta ba Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tsawaita dokar Zaman Gida Dole da mako daya.
Gwamnatin tarayya ta saka dokar hana walwala da zaman gida dole na makonni biyu a jihar Kano domin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
Kwamishinan Yada labarai, Muhammed Garba ya bayyana cewa gwamnati ta kara mako daya ne domin yin biyayya ga shawarwarin ma’aikatan kiwon lafiya na rage yawan gwamatsuwar mutane a jihar wadda shine hanya mafi girma da ake yada cutar.
Gwamnati tace tana ci gaba da aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
Bisa ga sanarwar, gwamnati ta yi kira ga mutane da su yi hakuri su bi doka da kiyaye hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.
Mutum 666 suka kamu da cutar Korona a jihar Kano, 63 sun warke, 32 sun mutu.