Gwamnatin Jihar Katsina ta zaftare kasafin kudin jihar na shekarar 2020.
Gwamnati ta rage kasafin jihar daga naira biliyan 244 zuwa naira biliyan 213 a dalilin karyewar farashin danyen mai da kuma annobar Korona Bairos.
Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya bayyana haka a lokacin da yake karbar sabon kundin kasafin kudin daga kwamishinan kudi na jihar Farouk Jobe ranar Alhamis a fadar gwamnatin jihar.
Masari ya ce majalisar jihar ta tattauna kuma ta amince da sabon kasafin kudin.
A karshe ya yi kira da a rika bin dokar da gwamnati ta saka domin kaucewa kamuwa da cutar Korona Bairos.