Kashi 90% na wadanda suka kamu da Coronavirus a Kaduna Almajirai ne da aka jijjibo daga Kano

0

Kakakin gwamnan jihar Kaduna Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa mafi yawan mutanen dake dauke da cutar Covid-19 a jihar almajirai ne da aka dawo da su daga jihar Kano.

Gwamnatin Kaduna ta ce a yanzu haka mutum 72 suka kamu da cutar, daga ciki 65 duk almajirai daga Kano, sannan kuma da wasu ‘yan sanda biyu da suka kamu da cutar suma.

Baya ga haka gwamnati ta ce ta gano cewa ‘yan sanada na daga cikin wadanda ke karya dokar hana tafiye-tafiye a kasar nan. Da su ake hada baki a karya doka.

“Mun samu labarin cewa akwai wasu Jami’an tsaro dake karya dokar hana tafiya daga wani jiha zuwa wani da gwamnati ta saka.

“Karya dokar da wadannan Jami’an tsoro ke yi na daga cikin dalilan dake yada cutar a jihar sannan da kawo koma a bayan ci gaban da aka samu wajen dakile yaduwar cutar a jihar.

Ya yi kira ga mutane da su guji karya dokar hana yin tafiya daga wannan jiha zuwa wani jihar.

Mutum 81 ne suka kamu da cutar a jihar.

Daga ciki 72 na kwance a asibiti, an sallami mutum 8, daya ya mutu.

Idan ba a manta ba a ranar Litini ne Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 170 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan.

Alkaluman da NCDC ta fitar ya nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 76, 37-Katsina, 32-Jigawa, 23-Kano, 19-FCT, 18-Borno, 10-Edo
9-Bauchi, 6-Adamawa, 5-Oyo, 5-Ogun, 1-Ekiti, 1-Osun, 1-Benue, 1-Niger, 1-Zamfara

Yanzu mutum 2802 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 417 sun warke, 93 sun
mutu.

Share.

game da Author