Kashi 90% na talakawan duniya fitik a surkukin daji suke samun abincin dogaro da kai -Rahoto

0

Wani rahoton hadin-guiwa da Kungiyar Abinci ta Duniya (FAO) ta fitar ranar wannan Asabar, ya nuna cewa kashi 90% cikin talakawa fitik na duniya, sun dogara da surkukin jeji ne wajen samun abincin dogaro da kan su.

Rahoton wanda FAO tare da hadin-guiwar Hukumar Kare Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) da kuma d kuma Kwamitin Kare Hakkin Dazuzzuka na UNEP suka fitar, ya tabbatar da cewa wadannan kashi 90% bisa 100% na talakawa fitik, “sun dogara da dazuzzuka ne wajen samun abinci, itacen girke-girke da sauran kayan dogaro da samun abinci, da suka hada har da naman jeji da sauran su.”

Mutum milyan takwas daga cikin wadannan rukunin jama’a, a Yankin Latin Amerika su ke.

Surkukin dazuka na taka rawa wajen samar da canjin yanayi, duk da dai wasu annoba da bala’o’in da ake fuskanta kan zama kalubale. Haka dai masana kimiyya suka bayyana.

Bincike Na Musamman: Akwai Surkukin Dazuka Milyan 34.8 a Duniya

Wani rahoton musamman na hadin-guiwa tsakanin Cibiyar Binciken Majalisar Tarayyar Turai da kuma Hukumar Kididdigar Dazuka ta Amurka, sun ce akwai akalla surkukin dazuka har milyan 34.8 a duniya.

Da rahoton ke bayanin girma da fadin dazuka, an ce akwai akalla daga mai fadin hakta daya har masu fadin hekta milyan 680.

Wannan a cewar rahoton, ya nuna akwai bukatar kare dazuka daga gurbacewa da zaizayewa har ma da daidaicewar da suke ci gaba da yi.

A kan haka ne hukumomin FAO da UNEP suka dauki gaban-gabarar aikin Majalisar Dunkin Duniya domin kokarin kare lalacewar muhalli da kare dazuka ta hanyar daina karkata ga burbatar yanayi a duniya.

Mista Dongyu ya ce idan ana so a kare dazuka daga gubacewar yanayi, to tilas canja fasali, hanyoyi da yanayin da milyoyin mutane a duniya suka dogara da samun abinci a cikin surkukin daji.

Ita kuma Ms Anderson cewa ta yi akwai bukatar su tabbatar da kare wadannan dazuka har ma da itatuwan cikin su daga duk wata barazana da suke fuskanta.

Sun ce ya zuwa cikin 2020, sun cimma kashi 17% bisa 100% na muradin su.

“Mun samu nasarar killace akalla kashi 30 bisa 100 na dazuka masu surkukin bishiyoyi, dazuka masara surkukin bishiyoyi da kuma dazukan da ke gefen teku a duniya.”

Share.

game da Author