Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa za a samu Karin mutane da yawa da zasu kamu da Coronavirus a jihar.
Ganduje yace hakan ya biyo bayan kakkafa sabbin wuraren yin gwajin cutar da gwamnati ta yi a jihar.
Bayan haka kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar kuma mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna yayi Kira ga mutane be da su dai na Yi wa cutar ganin da zarar ta Kama mutum shi ke nan Lahira Salamu alaikum. Sannan ya hori mutane da su ci gaba da bin dokokin gwamnati don kiyaye wa da ga kamuwa da cutar.
Haka kuma jagoran kungiyar kula da yaduwar cutar, Tijjani Hussaini ya Yi Kira ga wadanda suka kamu da cutar su rika zuwa yin gwaji, kuma su daina arcewa idan aka neme su zo a gwada.
Jihar Kano ce jihar ta biyu a Najeriya da cutar ta fi tsanani a Najeriya.
Sama da mutum 5000 sun kamu da cutar a kasar nan.