Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya rage albashin ‘yan siyasa da aka nada mukamai a jihar da kashi 50 bisa 100.
Sakataren yada labaran gwamnatin jihar Kano, Awwal Anwar ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Kano.
Anwar ya ce hakan ya biyo bayan karyewar tattalin arziki ne da aka samu da karancin kudaden shiga a dalilin annobar Korona.
” Saboda rashin samun isassun kudaden shiga yanzu a dalilin annobar Korona duka ‘yan siyasa da aka nada za su rika amsar rabin alabshin su ne daga watan Mayu. Hakan ya hada harda gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da mataimakin sa Nasir Gawuna.
” A dalilin Annobar Korona, da garkame gari da aka yi, kusan duka kamfanonin dake Kano basu aiki. hakan yasa ana samun karancin kudaden shiga.
Ganduje yace wannan rage albashi da gwamnati ta yi ya hada harda shugabannin kananan hukumomi da mataimakan su, kansiloli, masu bada shawara da dai duk wanda siyasa ce ta nada shi.