KANO COVID-19 – Gwamnati ba zata Iya karemu ba, sai mun bi ka’idojin kare kanmu don mu zauna Lafiya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Coronavirus a garin Kano ta zama kamar kurar da ta kwance a hannun mai ita. Cutar ta fantsama cikin al’umma. Tunda bincike ya nuna yanzu, a cikin samfuri na gwaji guda 100 na mutanen Kano za a iya samun 80 suna da cutar. Haka tsohon shugaban NCDC, Dr Nasir Gwarzo, ya bayyana a BBC Hausa. Hatta mutuwar da dattijai suke yi a jihar, Gwarzo yace akasari corono ce.

A baya, a cikin mutane dari zai wuya a samu mutum ashirin da cutar a jikinsu. Haka ne yasa lambobin mutanen da suke kamuwa basu da yawa a kowacce rana idan hukuma ta fitar da jadawalin cutar a Najeriya.

Mustapha Soron Dinki

Lokacin da cutar bata shigo jihar Kano ba, mutane da yawa sun yi harsashen yadda zata kasance a garin idan ta shigo. Rashin yadda da cutar, taurin kai, siyasa, gidadanci da rashin kan-gado suna daga cikin abunda masana suka tabbatar da zai iya baiwa annobar damar fantsama a Kano. Lallai idan anki ji, to ba za a ki gani ba, idan kuwa an gani, ba za a ga da kyau ba.

Sakwasakwa da gwamnatin Kano da ragowar jihohin Najeriya suka yi da dokar zaman-gida-dole baya nufin talaka ya saki jikinsa kamar cutar ta tafi. Tana nan a labe, tana neman wadanda zata cafka idan Allah yaso. Wannan ya faru shekaru da yawa a baya, lokacin annobar “Spanish flu”. Bayan Gwamnatocin duniya sun sako mutane suna ta murna, ita kuma cutar sai ta samu damar kara kama mutane sosai. Hakan yasa cutar taci mutane masu yawa a lokacin. Matsalar rashin tallafawa mutane yadda yakamata ce take damunmu a kasarmu.

Misali, Gwamnatin Kano ta bayar da Litinin da Alhamis don wasu kasuwanni da shaguna su gudana. Wallahi kada ka kuskura ka kafircewa bin ka’idojin kare kai. Irinsu yin amfani da takunkumin fuska, yawan wanke hannu da kuma yin nesa-nesa da juna.

A halin da Kanawa suke ciki yanzu, babu maganar karyata cutar saboda karyata abunda ya tabbata baya daga cikin siffofin mutane masu ilimi na addini da na zamani. Wasu suna zargin shugabanni da zuzuta cutar don su samu kudi. Kaddara ma haka ne, tunda ta tabbata akwaita kuma gashi har ta kashe babban mutum daga cikin masu mulki, dole talaka shima ya shiga taitayinsa.

Allah ya karemu.

Share.

game da Author