KANO: Cikin almajirai sama da dubu da aka yi wa gwaji, 28 ne kacal ke dauke da Korona – Garo

0

A ranar Laraba gwamnati jihar Kano ta bayyana cewa mutum uku sun mutu a dalilin fama da suka yi da cutar Covid-19.

Zuwa yanzu mutum 41 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a jihar.

Ma’aikatar kiwon lafiyar jihar ta ce an sallami mutum daya da ya warke daga cutar da hakan ya kawo adadin yawan mutanen da aka sallama zuwa 135.

Ma’aikatar bata kara bada haske kan yawan mutanen da suka rasu ba da yawan da aka sallama ba a jihar sai dai kuma hukumar jihar ta ce mutum 936 ne ke dauke da cutar a jihar.

Sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna cewa an samu karin mutum 389 da suka kamu da cutar a kasar nan, jihar Kano na da mutum 13.

Almajirai 28 sun kamu a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sanar cewa almajiran 28 sun kamu da cutar a jihar.

Shugaban kwamitin maida da almajirai jihohinsu na asali na jihar Murtala Garo ya Sanar da haka a zaman da kwamitin yaki da Covid-19 ta yi ranar Laraba.

Garo ya ce gwamnati ta yi wa almajirai 1,146 gwajin cutar inda sakamakon gwajin cutar ya nuna cewa 28 na dauke da cutar.

Ya kuma ce almajirai 311 daga cikin 1,146 da aka yi wa gwaji na dauke da wasu cututtuka da suka hada da zazzabin cizon sauro, kiwon ciki, zazzabi da sauran su.

“Gwamnati ta mayar da almajirai 419 zuwa jihar Katsina, 524 zuwa Jigawa, 155 zuwa Kaduna, 38 zuwa Bauchi sannan 36 zuwa Gombe.

“Jihar ta kuma karbi almajirai 179 daga Adamawa, 220 daga Nassarawa, 96 daga Gombe, 18 daga Katsina sannan 92 daga Kaduna.

Garo ya ce gwamnati ta maida almajirai 723 zuwa ga iyayensu sannan nan ba da dadewa ba gwamnati za ta saka wadannan yara a makarantun boko domin samun ilmi na zamani.

Canja tsarin makarantun almajiranci a jihar

A zaman da kwamitin yaki da Covid-19 na jihar ta yi gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya Sanar cewa gwamnati ta shirya sabbin tsare-tsare da zai da arika koyar da yara boko da atabi maimakon Allo kawai.

Ganduje ya ce wannan shiri zai taimaka wajen samar wa duk yara a jihar ilimin boko.

“Idan wani cikin malaman almajirai ya dage sai ya ci gaba da koyar da almajirai gwamnati ta ce dole sai ya kawo tsarin darusan da zai koyar wa yaran, ya tabbatar cewa yana koyar da darusan turanci, lissafi da sana’o’in hannu.

“Sannan ya samar wa yaran ingantacen wuraren kwana da abinci tare da yi wa daliban jarabawa kafin gwamnati ta amince da haka.

Share.

game da Author