KANJAMAU: Akwai yiwuwar mutum sama da 500,000 za su mutu dalilin maida hankali da aka yi kan Korona a Nahiyar Afrika

0

Hukumar samar da tallafi na Majalisar dinkin Duniya (UNAIDS) da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) sun ce kididdiga ya nuna cewa Nahiyar Afrika za ta rasa masu fama da cutar Kanjamau akalla 500,000 za su iya rasa rayukan su a dalilin annobar cutar Korona.

Sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa kasashen dake yankin Kudu da Sahara sun dakatar da siyo magungunan cutar kanjamau na tsawon watanni 6.

Binciken ya kuma nuna cewa masu fama da cutar kanjamau 470,000 ne suka mutu a Kudu da Saharan Afrika a shekaran 2018 a dalilin rashin samun magani.

A yanzu dai wasu kasashen Afrika sun maida hankali wajen siyo magungunan duk da fama da dakile yaduwar cutar Korona da suke yi.

UNAIDS ta tallafa wa wasu kasashen da magunguna irin haka da suka kare musu ko kuma ta yi musu karanci, kamar Kamaru da Bostwana.

A kasar Kongo kuma masu Kanjamau ba su iya zuwa asibiti ba saboda dokar hana walwala da ka saka don dakile yaduwar Korona.

A yanzu dai kasashe 10 a Kudu da Saharan Afrika sun dakatar da shirin dakile yaduwar kanjamau Saboda coronavirus.

Jami’ar UNAIDS Winnie Byanyima ta ce kasashen Kudu da Saharan Afrika za su salwantar da ci gaban da suka samu wajen hana yaduwar kanjamau a dalilin yaki da cutar Covid-19.

Share.

game da Author