KAN IYAKAR NAJERIYA DA BENIN: Inda jami’an tsaro ke zubar da kimar su, su na taimaka wa masu karya dokar hana tafiye-tafiye saboda Coronavirus

0

Da jijjifin safiya na fita gida domin a matsayi na na mai rahoto a jarida, na gane wa ido na yadda dokar hana tafiye-tafiye ke aiki a kan kan iyakokin da Najeriya ta hada ruwa da wasu kasashen Afrika ta Yamma.

Kada a manta a ranar da Shugaba Mujammadu Buhari ya rufe filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa da kan iyakokin kasar nan, a ranar 23 Ga Maris, wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya su 36 ne kacal.

A ranar 30 Ga Maris, ranar da Buhari ya rufe Lagos, Abuja da Ogun, mutanen da suka kamu da cutar sun kai 140.

Daga nan kuma zai binciken PREMIUM TIMES ya nuna cewa jama’a na karya dokar hana tafiye-tafiye, inda ake zirga-zirga, lodi, jigila da karakaina ta cikin ruwa, tsakanin Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar.

Jami’an tsaron Najeriya ne ke dauke gindin wannan harkalla ta hanyar karbar cuwa-cuwa a hannun matafiya, su kauda ido su kyale mai shigowa ya shigo, mai fita ya fita.

Da Dan Gari A Kan Ci Gari:

Ga duk mai son tafiya Jamhuriyar Benin daga Lagos, abin da kawai zai yi farko shi ne ya tabbatar ya tashi ya fice daga gida, tun da asubahin farko. Sannan kuma ya tabbatar akwai kudade aljihun sa, wadanda zai rika zarowa ya na damka wa jami’an tsaro. Saboda duk inda ya samu shingen jami’an tsaro, aikin su kawai shi ne karbar kudi. Shi kuma matafiyi, aikin zaro kudi aljihu ya na bayarwa, ya same shi kenan.

A farkon watan Mayu, na fita da asubahi da nufin zuwa Benin, domin gane wa ido na irin yadda jami’an tsaro ke tsula tsiyar karbar kudade su na kyale ko m wane ya shigo ko ya fita ya dawo da abin da ya ke so ya shigo da shi.

Na bar gida a unguwar Ajah, misalin karfe 6 na safe, na nufi CMS, inda gada can ne mu ka rankaya.

A Saida Rai A Nemo Suna:

Ba mu dade da fara lulawa a cikin ruwa ba, sai rana ta fara fitowa, hasken ta da rika sa ruwan da mu ke tafiya a kai ya na wani sheki. A gefe kuwa Ga masu kwale-kwale da kananan jiragen ruwa nan sai hada-hada ake yi, ta fara aikin safe.

Idan ka na da nauyin aljihu, za a iya daukar hayar karamin jirgi a naira 20,000. Inda za a ajiye ka a wata tashar jirgin ruwa, wai Liverpool da ke yankin Apapa. Daga can kuma za ku shiga wani jirgin ruwan ku lula Gbaji, da ke yankin Badagry.

Duk wancan bayani fa matafiya ne masu nauyin aljihu. Ni da ya ke doguwar hanya na bi, inda marasa galihu su ke bi, sai da mu ka yada zango taahoshin ruwa uku kafin mu shiga Jamhuriyar Benin.

Kushewar Badi Sai Badi:

Daga CMS na biya naira 500, aka cusa mu kan wani dan kwale-kwale na katako, ku 20. Mu ka nausa, sai da mu ka yi tafiyar awa daya cur a cikin teku. Bayan mun yi nisa na tambayi direban cewa ya na ga babu mai rigar hana fasinja nutsewa cikin ruwa!

Direban ya yi min kallon-raini, ya ce min wa zai ba fasinjan naira 500 rigar hana nutsewa a cikin ruwa. Na ga mutanen da ke cikin kwale-kwalen babu ma wanda ya damu. Su ka ce ai babu komai, na kwantar da hankali na. Lafiya kalau za mu sauka. A haka dai har mu ka isa tashar Sagbokoji igiyar ruwa ba ta fara juj-juyawa ba.

Daga Sagbokoji mu ka hau wani karamin jirgin aka caji kowa naira 1,000, a tafiyar da ba ta wuce minti 15 ba. A wannan karamin jirgin hankali na ya dan kwanta, domin an bai wa kowa rigar hana nutsewa a cikin ruwa. Sannan kuma ya na da inji, ba tukin c-da-karfi kato ke yi ba.

‘Liverpool’, Tashar Da Ba Su San Akwai Coronavirus A Duniya Ba:

Mu ka sauka Liverpool, amma abin da zai ba ka mamaki, sai ka rantse d Allah ka ce mutanen wannan wuri ba a karkashin Jihar Lagos su ke ba. Jama’a sai hada-hada da rincimin karakainar kokarin hawa kananan jirage ake ta yi. Babu ruwan su da yin kaffa-kaffan gudun daukar cutar Coronavirus daga jikin wani.

Lahira Kusa: Yadda Na Shafe Awa Uku A Tsakiyar Teku:

An yi lodin mu cikin wani karamin jirgin ruwa, wanda aka rubuta wa “God Bess” a jikin sa. Mu 16 ne a ciki, kowa ya lalo naira 2,000 ya bayar.

A ciki n mu har da wata mata mai suna Iya Anu, wadda ta ce min ai ita kowane mako sai ta shiga Jamhuriyar Benin ta sayo kaya, duk kuwa da dokar hana tafiye-tafiye da aka kakaba.

An bi mu kowanen mu an ba shi rigar hana nutsewa a ciki n teku. Sai Any, yarinya ‘yar Iya Anu mai shekaru biyar ce kadai ba a bai wa rigar ba. Kwandastan mai suna Alaba ne ya ce ba su da rigar kananan yara.

Bayan Alaba ya biya ‘yan kamasho da ‘yan ka-yi-na-yi da ‘yan gargar. Sai ya ce mana to kowa ya kimtsa za a lula.

Ya kalle ni ya ce, “kada ka ji tsoro. Wannan jirgin ruwa ba, amma mai gudun tsiya, ba kwale-kwale ba ne.

Mun yi tafiya kamar ta minti 15, sai hadari ya taso. Kawai sai igiyar ruwa ta fara murdawa. Ina jin tsoron kai na, amma kuma ina jin tsoron ga karamar yarinya, Anu mai shekaru 6, ita babu rigar hana nutsewa a cikin ruwa.

Sauran fasinja kuwa na ga ba su ma damu ba da yadda igiyar ruwa ke kadawa, ruwa na yin toroko. Sai na ga karamar yarinya Anu had mika hannu ta ke yi ta na wasa da ruwa.

Ba zato kawai sai jirgin ya rage gudu, saboda inji daya ya lalace. Direban ya ce mana za mu dan kara bata lokaci kafin mu isa.

Yayin da igiyar ruwa ta rika kadawa da karfi, sai fasinjoji su ka fara kiran sunan Ubangiji. A haka dai mu ka karasa tashar Gbaji, kowa ya fita ana jinjina wa Alaba direban jirgin.

Kowa Ta Sa Ta Fisshe Shi: Na Hau Okada Naira 1,500 Daga Gbaji Zuwa Seme:

Mu na sauka daga jirgin ruwa sai ‘yan Okada suka kewaye mu. Yawancin su ma ‘yan Jamhuriyar Benin ne, ba Turancin kirki su ke ji ba. Na dubi wani mai dan dama-dama, na ce shi zai dauke ni. Ya ce ba matsala.

“Amma zan ba ka shawara, duk inda mu ka ga jami’an tsaro, ka dake kawai, ka yi fuska. Kada ka nuna kai bagidaje ne a wannan harka. Ka nuna kai ma dan duniya ne.”

Ya ce min a wasu wuraren ma ba lallai mu samu jami’an tsaro ba. Saboda su ma sun boye, tsoron Coronavirus su ke yi.

Jami’an Tsaro Ko Dai Jami’an Karbar Cin-hanci!:

Daga Gbaji a Badagry zuwa bakin ‘boda’, sai da lissafa shingen jami’an tsaro 28. Kama daga na ‘yan sanda, kwastan, sojojin da ‘jami’an shige-da-fice. Babu ruwan su da maida hankali kan aiki, sai dai karbar kudade.

A gefe kuma ga motocin sintiri na jami’an tsaro, amma direban babur din nan sai dai ya daga musu hannu su dago masa. Ko ma dai me kenan, to akwai sanayya a tsakanin su.

Na Sake Haduwa Da Iya Anu Bakin ‘Bodar’ Shiga Benin:

Dan okada ya dauke ni bakin ‘boda’. Ga mutane dankam, ya ce min, “kada ka yarda ka nuna kan sabon-yanka-rake ne. Ya shiga cikin gungu ku shige kawai. Idan ka yi sa’a ba za a tsayar da kai ba.

Dubawar da zan yi sai ga Iya Anu, tare da Anu da jarkoki biyu, amma babu komai cikin su. Ta ga kamar na dan daburce, sai ta ce ba kwantar da hankali na, za ta taimake ni. Sai ta miko min jarka daya, ta ce na rike kawai.

Duniya Sai Da Kwana, Idan Ka Tafi Tsaye Sai A Gan Ka:

Iya Anu ta ce min, “Akwai wata kwaya cikin walet din ka?”

Na ce mata “a’a.

Ta ce, “to duk inda mu ka isa ga jami’an tsaro, kada ka kurkura ka yi magana. Ko tambayar ka aka yi, ni zan bayar da amsa.”

Mu ka isa shingen wasu amma su sanye da kaki, su na buga wasan lido. Aka tambaye mu:

“Daga ina ku ke?”

Iya Anu ta ce, “Haba oga, wannan tambaya sai ku ce ba ku san ni ba! Gida zan wuce tare da dan uwa na.”

Ta zaro naira 200 ta rika musu. Ni ma na zaro na mika, suka karbe, mu ka shige. Bayan mun yi gaba ta ce min jami’an kwastan ne!

Abin mamaki, na biya naira 200 na shiga Jamhuriyar Benin a lokacin da aka haramta tafiye-tafiye a Lagos, Abuja da Ogun, saboda Coronavirus.

Yadda Jami’an Tsaro Ke Tsula Tsiyar Karbar Kudade A Ruwa, Hanyar Shiga Lagos Daga Jamhuriyar Benin

A takaice dai bayan mun shiga Benin, Iya Anu ta taimaka min na yi canjin kudi a Ajase Topa. Nan na zauna, na huta. Da dare na kewaya garin, na yi ‘yan yawace-yawace, duk kuwa da cewa ba Turanci su ke ji ba.

Ba Hawan Ba Saukar – Hawan Bishin Kutare:

Dawowa Najeriya kafin isa Lagos ya fi wahalarwa matuka. Aka dauko ni zuwa boda dauke da sumogal din buhun shinkafa da sugar.

Muka wuce babu wata tsangwama. Daga Owodi zuwa Gbaji sai da na kirga shingen jami’an tsaro 28.

A bakin kogi ga fasinjoji nan, kowa dauke da kayan sumogal iri daban-daban. Aka loda mu a karamin jirgi, sannan aka cusa kayan sumogal a karkashin kujerun da mu ke zaune.

Ana maganar jami’an tsaro sai wata fasinja ta ce ai duk wani jami’in tsaro ya san kayan sumogal ake daukowa. Daga baya na gano ashe yawancin shinkafar da ke cikin jirgin ruwan duk ta matar ce.

Yadda Sojojin Ruwa Kwastan, Sojojin Ruwa Da ‘Yan Sanda Ke Karbar Kudade A Tsakiyar Ruwa:

Duk wadanda mu ke cin karo da su, babu wanda ya makala sunan sa a jikin kakin sa.

Sau uku sojojin ruwa na tare jirgin mu. Sai hudu ‘yan sandan ruwa na tare mu. Sai daya kwastan suka tare mu duk a cikin ruwa.

Gaba daya dai a wadannan wuraren mun kashe jimillar naira 22,000 toshiyar-baki.

Akwai wurin da wasu sojoji uku suka bi mu a cikin ruwa a sukwane. Su ka ce za au harbi direban mu idan bai tsaya ba. Bayan ya tsaya suka tambaye shi dalilin da ya ki tsayawa. Ya ce bai gan su ba.

Daya daga ciki n su ya yi tsalle ya shigo cikin jirgin mu. Bayan ya duba, ya kwala wa ogan su kira ya ce, “kayan sumogal su ka dauko. Sai sun biya naira 20,000.”
Da kyar da magiya mu ka roke su suka karbi naira 5,000.

Dan Sanda Abokin Kowa:

Wato ‘yan sandan da ke sintiri a kan ruwa, ba su da bambanci da wadanda ke ciki n gari. Ba su yi maka buyagi ko tashin-tashina. Sai dai idan aka tare ku, za a gaishe ku, a ce “da wace tsaraba ku ka zo mana da ita. Su karbi abin sa za su karba ku yi gaba.

Masu taurin sasantawa sai jami’an kwastan. Da wasu suka damke mu da jirgin da mai jirgin mun kwashe sama da minti 30. Wani ya shigo ya karbe makulli a hannun direba. Ya kai wurin ogan su. To daga nan da aka fara ciniki da roko da ban-baki.

Ana cikin haka sai wani ya ce mu mike tsaye kowa ya daga hannu. A nan ne fa ana caje ni, sai aka ga na’urorin rikodin din bidiyo da bayanai. Aka ce min me na ke yi da su? Na ce ni dalibi ne, na Jami’ar OAU, na kwafi ayyukan kundin digiri ne zan kai makaranta idan an koma aiki.

A nan katsahan sai ga wani karamin jirgin ruwa a guje. Su ka yi sauri su ka koma kan sa. Su ka sallame mu, saboda sun ga inda mai dan maiko ya ke.

To a cikin wannan hanzarin ne suka manta ba su miko min daya daga cikin na’urorin daukar bayanai da bidiyon ba.

Bayan wakilin mu ya dawo, PREMIUM TIMES ta bi dukkan jami’an yada labarai na hukumomin tsaron domin jin ta bakin su. Wadanda suka nemi hujja kuma duk an tura musu. Amma daga wadanda ba su sake cewa komai ba, sai wadanda suka ce za su yi bincike.

Share.

game da Author