Kada korona ta hana ku shayar da ‘ya’yan ku nono – Kira ga Iyaye

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi kira ga mata uwaye da su juri shayar da ‘ya’yan su nono koda sun kamu ko kuma suna zargin sun kamu da cutar Covid-19.

WHO da UNICEF sun yi Wannan kira ne a shafukan su dake yanar gizo domin yin tuni ga uwaye mata mahimmacin shayar da ‘ya’yansu nono maimakon bai wa jarirai madaran gwangwani.

Kungiyoyin biyu sun kara da cewa sakamakon bincike ya nuna cewa mace dake dauke da cutar Covid-19 na iya shayar da danta nono ba tare da dan ya kamu da cutar ba.

Kungiyoyin sun ce yin Wannan kira a Wannan lokaci da duniya ke yaki da annoban cutar Covid-19 na da muhimmancin gaske ganin yadda kamfanonin dake sarrafa abincin jarirai ke amfani da Wannan lokaci domin tallatar da abincin jarirai ga mata a kasashen duniya.

“A yanzu haka matakan hana yaduwar cutar coronavirus da aka dauka da suka hada da rage cunkoso na daga cikin matsalolin dake hana mata Shayar da ‘ya’yan su nono.

Bisa ga ka’ida kamata ya yi mace ta Shawara da danta nono zalla na tsawon watanni shaida domin bukasa garkuwan jikinsa.

Likitoci sun ce karfafa karfin garkuwan jariri na zama kariya garesa daga kamuwa daga cututtuka sau 14 fiye da jariran da aka raine su da abinci da kamfani ke sarrafawa.

WHO da UNICEF sun yi kira ga gwamnati kasashen duniya da su zage damtse wajen hana sarrafa abincin jarirai da wadannan kamfanoni ke yi tare da hana shigowa da abincin kasashen su.

Sun kuma ce bai kamata kasashen duniya su karbi tallafi ba daga wajen kamfanoni irin haka ba musamman a wannan lokaci da duniya ke yaki da annoban cuta ba.

WHO da UNICEF sun fitar da hanyoyi da mata za so kiyaye wajen shayar da ‘ya’yan su nono domin kare su daga kamuwa da cutar Covid-19.

Ga hanyoyin

1. Mace ta wanke hannayenta da ruwa da sabulu ko kuma da sinadarin tsaftace hannu kafin ta dauki da ko ‘yarta.
2. A yi amfani da takunkumin rufe fuska a duk lokacin da mace za ta dauki ko shayar da da ko ‘yarta nono.
3. A yi tari ko atishawa a gwiwar hannu ko kuma a yi amfani da tissue.
4. A tsaftace muhalli domin guje wa kamuwa da cutar.
5. Mace za ta iya kiyaye sauran sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar koda bata da takunkumin rufe baki da hanci.

Share.

game da Author