Majalisar Tarayya ta yi suka kan yadda gwamnonin kasar nan ke maida Almajirai jihohin su na asali, majalisar na mai cewa yin haka tauye wa Almajiran hakkin su ne na zama ‘yan kasa.
Honarabul Aisha Dukku, daga jihar Gombe ta jagoranci muhawara akan haka a zauren majalisar tarayya ranar Lahadi.
Aisha Dukku ta ce maida almajiran jihohin su na asali karya dokar kasa ce da ya ba kowanni dan kasa damar zama ako-ina a fadin Najeriya.
Sannan kuma ta ce yadda ake gwamatsa su a motoci cikin tsananin zafin rana a yi dogon tafiya dasu shima bai kamata a rika haka ba.
Majalisar ta amince da a tilasta wa gwamnoni su dakatar da jigilar almajiran da suke yi zuwa jihohin su na asali sannan su janye shawarar dakatar da almajirci da barace-barace a jihohin su har sai sun shirya saka Alamjirai duka a tsarin karatu na UBEC.
Idan ba a manta ba gwamnatocin Arewa sun yarda su maida Alamjiran jihohin su saboda matsalar annobar Coronavirus. Tunda aka fara wannan aiki na maida almajirai, an rika samun da yawa daga cikin su dauke da cutar Coronavirus.
Hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin wasu gwamnoni da suke ganin wasunsu na yin siyasa da abin. Jihohi da dama musamman Kaduna, Gombe da Kano sun koka cewa yawa-yawan Almajiran da aka dawo musu dasu ne yasa suka samu yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus.