Gwamnan Jihar Bauchi da ya dage cewa ba zai saka dokar hana walwala a jihar sa ba kamar yadda wasu jihohin suka yi don dakile yaduwar Coronavirus, ya kakaba dokar a kananan hukumomi uku.
Hakan ya biyo bayan samun karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Jihar da aka yi a cikin kwanakin nan.
A cikin awa 24, an samu karin mutum 66 da suka kamu a jihar Bauchi da hakan yasa dole aka saka dokar hana walwala a wasu kananan hukumomin jihar.
Yanzu Jihar Bauchi na da mutum 183 da suka kamu da cutar Coronavirus.
Gwamna Bala ya ce cutar ta fi tsanani a yankin Katagum inda mutum 63 cikin adadin yawan wadanda suka kamu duk ‘yan wannan yanki ne. Sannan ya koka kan yadda mutane suka rika tururuwa daga Kano zuwa kasar Katagum da wannan ne sanaiyyar yada cutar.
Gwamna Bala ya ce an garkame kananan hukumomin Katagum, Giade da Zaki na kwanaki 10 domin dakile yaduwar cutar, kuma kuma za a hukunta duk wanda ya karya wannan dokar ko shi waye.
Idan ba a manta ba an yi ta ruwaito wa cewa mutane na ta mutuwa a yankin Azare. Sai dai daga baya kwamitin dakile yaduwar cutar Coronavirus karkashin mataimakin gwamna Baba Tela, ya musanta haka, inda daga baya dai kuma ya samu tabbaci a rubuce cewa ana bizne mutum akalla shida duka awa daya a jihar.
A karshe gwamna Bala, ya ce lallai ya samu rahotan mace-mace da aka yi har mutum 150 da suka rasu a sanadiyar wata cuta da ba a san wacce iri bace.
Gwamna Bala ne mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a Jihar Bauchi. bayan makonni da ya dauka a killace, Allah ya bashi lafiya.