Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oin kasar nan JAMB ta bayyana cewa a jihohin Kaduna, Imo da Anambra dalibai suka fi satar Jarabar JAMB.
Sauran jihohin kuma da suma aka samu suna da dalibai da aka samu sun yi satar ansa sun hada da Enugu da Jihar Filato.
Dalibai 1,945,983 suka zauna jarabawar JAMB a 2020.
Ba a samu koda mutum daya da yake satar ansa a jarabawar bana ba a jihohin Bayelsa, Katsina, Kebbi, Niger, Taraba da Zamfara.
A jihohin Adamawa, Gombe, Sokoto da Yobe, mutum daya kacal aka samu.
Jihohin kudu sun fi yawan wadanda suke satar ansa a jarabawar bana fiya da jihohin Arewacin Najeriya.
Baya ga satar ansa, an akam wasu a dalilin yin dabanci a wuraren jarabawa, buga takardun jarabawa na karya da kuma wadanda suka yi rajista sau biyu.