Jihar Taraba ta janye dokar hana Sallar Juma’a da zuwa Coci ranar Lahadi

0

Mataimakin gwamnan Jihar Taraba Haruna Manu a jawabi da yayi wa mutanen jihar ranar Litini ya bayyana cewa gwamnati ta janye dokar hana salloli da zuwa coci a jihar.

Manu yace daga yanzu za a rika walwala a ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi. Kowa zai wataya a je masallacin juma’a ranar Juma’a sannan kiristoci su tafi Coci ranar lahadi.

Manu ya kara da cewa doka na nan a ranakun Litinin, Talata, Laraba da Alhamis, kuma duk wanda ya karya doka zai dandana kudar sa.

Idan ba a manta ba a jihar Kano, gwamna Ganduje ya janye dokar hana sallar Juma’a sannan kuma ya amince musulmai su halarci sallar Idi ranar Asabar ko Lahadi.

Kakakin gwamnatin jihar Kano, Salihu Tanko ya shaida cewa gwamna Ganduje ya gana da manyan malamai 30 a jihar na sama da awa biyu. A karshen ganawar gwamnatin jihar ta amince amince a janye dokar hana sallar juma’a a jihar sannan kuma idan Allah ya kai mu ranar Asabar ko Lahadi za a yi sallar idi.

” Gwamnati ta amince al’umma su halarci sallar Idi ranar sallah a duk fadin jihar. Sai dai ya ce a bi ka’idojin da gwamnati ta saka domin kiyaye kamuwa da cutar Korona.

” An umarci Malaman Masallatan Juma’a da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka takunkumin fuska ya kuma wanke hannaye da saka sanadarin tsaftace hannaye sannan a raba sahu kuma kuma a saka jami’an hizba su tabbata an bi wadannan dokoki.

Share.

game da Author