Kwamishinan Al’adu da yawon Shakatawa na Jihar Nasarawa, Dogo Shammah, ya bayyana cewa gwamnan jihar Abdullahi Sule ya amince a janye dokar hana sallah a masallatai da ibadar coci na makonni biyu a jihar.
Dogo ya ce gwamna Sule ya gindaya wasu sharudda da dole sai masallata da kiristoci sun bi a lokacin da aka janye wanna doka.
” Kowa zai saka takunkumin fuska, sannan kuma za a saka man tsaftace hannaye da yin feshi a wuraren ibada da kuma yin nesa-nesa da juna.
Bayan haka kuma ya ce idan makonni biyun suka cika gwamnati za ta duba yanayin yadda jama’a suka yi biyayya da dokar sanna ta sake sanar da sabbin matakai.