Jihar Legas ta tara kudaden shiga fiye da jimlar na jihohin Arewa 19 kaf din su a 2019 – NBS

0

Hukumar Kididdiga ta kasa NBS ta bada rahoton cewa jihohin Legas, Ogun, Babban Birnin Tarayya, Abuja da jihar Ribas sun tara kudin shiga fiye da jimlar kudaden shiga da jihohi 34 suka tara kaf din su a 2019.

A bayannan rahoton, jihar Kaduna ce ta fi kowacce jiha a arewacin Najeriya tara kudaden shiga a shekarar 2019, Inda ta tara sama da naira biliyan 44, sai kuma jihar Kano da ta tara naira biliyan 40.

Sannan kuma a cikin jimlar naira tiriliyan 1.3 da jihohi suka tara, jihar Legas kawai ta tara fiye da abin da duka jihohin Arewacin Najeriya suka tara, tun daga jihohin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya har da Abuja.

Kuma jihohin Legas, Ogun, Ribas da Abuja sun tara fiye da jimlar abin da duka jihohi 34 suka tara a 2019.

A can kasa kuwa, Jihar Taraba ce tafi tara kudaden shiga maki karanci a kasar nan inda ta iya tara naira biliyan 6.5 ne kacal a shekarar 2019. Daga ita sai jihar Gombe da ita ma naira biliyan 6 ta iya tarawa, sai kuma jihar Kebbi da ta tara naira biliyan 7 da yan kai.

Daga su sai jihohin Barno, Katsina, Yobe, Ekiti da duk suma dai irin haka suka tara.

A rabon da gwamnatin Tarayya tayi wa jihohi kuwa a shekarar 2019, jihohin Delta, Ribas, Akwa-Ibom, Bayelsa da Legas be suka samu kaso mafi tsoka a rabon.

Gwamnatin Tarayya ta rabawa jihohi naira tiriliyan 2.3 a shekarar 2019.

Jihohin Legas, Ogun da Abuja ne suka iya tara fiye da kason su da gwamnatin Tarayya ta basu a shekarar, 2019.

Sai kuma jihohin Ribas, Kwara da Kaduna da suka tara fiye da Rabin kason da gwamnatin Tarayya ta basu a 2019.

Share.

game da Author