Jihar Kaduna ta rasa naira biliyan 6 kudin shiga saboda coronavirus – Gwamnati

0

Shugaba hukumar kula da kasuwannin jihar Kaduna Muhammad Bayero ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta rasa naira biliyan 6 kudin shiga a cikin wata daya a dalilin Coronavirus.

Bayero ya ce garkame jihar da aka yi a dalilin annobar coronavirus, ya sa ba a samun kudin shiga daga kasuwannin jihar da ya da yanzu haka jihar ta rasa naira biliyan 6 cikin wata daya.

Ya ce gwamnati ta kafa kasuwannion wucin gadi a amakarantun firamaren jihar domin mutane su rika zuwa a kwanakin da aka bada don siyan abinci su garzaya su siya abinci a wadannan kasuwanni.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kasuwannin wucin gadi a makarantun firamaren jihar domin mutane su rika zuwa a wadannan ranaku suna siyan abinci.

Bayero ya ce anyi su kusa-kusa ne domin rage wa mutane wahalar dogon tafiya zuwa manyan kasuwanni dake kulle.

” Duk wanda zai shiga wadannan kasuwanni sai an yi masa gwaji a kofa. Sannan nesa-nesa za a rika kasuwanci. Duk wanda ya kar ya dokar yin nesa-nesa da juna zai kuka da kansa.

” An saka jami’an tsaro a kowanni kasuwa domin tabbatar da an bi doka. ”

A karshe Bayero yayi kira ga mutanen jihar da su bi doka domin a iya dakile yaduwar cutar.

” Idan aka bi doka za a iya samun sauki cikin watanni uku maimakon ace an garkame jihar kwata-kwata na shekara daya sabo da mutane sunki bin doka.

Share.

game da Author