Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa wata tsohuwa mai shekaru 98 da mutum 25 sun warke daga cutar Coronavirus a jihar.
Sanwo-Olu ya rubuta haka ne a shafin sa ta tiwita ranar Laraba.
Ya ce adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar ya kai 528.
“An sallami mata 13 da maza 13 daga asibitocin kula da masu fama da coronavirus dake jihar.
“Yayin da ma’aikatar kiwon lafiya ke sadaukar da rayukansu wajen kula da masu fama da cutar kamata ya yi mutane su kiyaye hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Bisa ga sanarwan da Hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba mutum 2,006 ne suka kamu da cutar a jihar.
Yanzu haka mutum 1,427 na kwance a asibiti, mutum 528 sun warke daga cutar sannan 34 sun mutu.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas Akin Abayoymi ya bayyana cewa daya daga cikin ‘yan Najeriya da aka dawo da su daga Dubai ya rasu bayan yayi fama da cutar Coronavirus.
Abayomi ya ce ma’aikatar kiwon lafiya jihar bata tabbacin ko cutar ne ta yi jikinsa saboda har yanzu sakamakon gwajin cutar da aka yi wa mutumin bai fito ba.
Ya yi kira ga mutane da su tsaftace muhallin su da jikinsu, tsagaita tsayuwa kusa da mutane sannan da amfani da takunkumin kare fuska domin guje wa kamuwa da cutar.