Jaririya ‘Yar wata Hudu ta kamu da Korona a Kaduna

0

Kwamishinan kiwon Lafiyar Kaduna Amina Baloni ta ce jaririya ‘ya wata Hudu ta kamu da cutar Coronavirus a Kaduna.

Baloni ta ce iyayen wannan jaririya su kawo yar asibiti domin a duba ta kan matsalar yankewar numfashi da tafe fama da shi. Bayan likitoci sun yi mata gwaje-gwaje sai sakamakon gwajin ya nuna ta kamu ne da Korona.

Bayan haka kwamishina Amina ta shaida cewa mahaifin wannan jaririya tana ya yi ta balagoro daga kaduna zuwa kano a ‘yan kwanakinnan. Suma iyayen nata an dibi jinin su domin yi musu gwajin cutar.

Bayan haka kuma Amina ta bayyana cewa mutum ashirin da suka kamu da cutar a ranar juma’a duk yan uwan wadanda suka kamu da cutar ne a abaya da aka yi musu gwaji.

Ta ce A karamar hukumar Chikin kawai an samu a gida daya mutum biyar duk sun kamu da cutar, sannan akwai wasu hudu a karamar hukumar giwa. sai kuma mutum Uku a Kaduna ta Arewa, daya a Sabon Gari, Igabi da Kaduna ta Kudu.

” Ina so in yi kira ga mutane da su rika nesa-nesa da bakin da zasu rika ziyartar su domin daya daga cikin dattijon da ya kamu da cutar ya kamu ne a dalilin bako da ya zo masa yana dauke da cutar bai sani ba.

Ta hori mutane da su ci gaba da wanke hannayen su da ruwa da Sabulu, sannan a rika goge hannu da man taftace hannu.

Korona ta yadu a kananan hukumomi 9 a fadin jihar da suka hada da Igabi, chikun, Kaduna Ta Arewa, Kaduna Ta Kudu, Sabon Gari, Giwa, makarfi, Soba.

Share.

game da Author