Ina nan da rai na cikin koshin lafiya, ban mutu ba – Ghali Na’abba

0

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na’abba ya bayyana cewa yana nan da ran sa bai mutu ba kamar yadda wasu jaridan Najeriya suka yi ta yadawa wai Allah yayi masa Rasuwa.

Honarabul Ghali ya ce ya kasar Birtaniya yanzu haka kuma rashin jirgi ne yasa bai samu damar dawowa kasar nan ba, ya makale a can birnin Landan.

” Na gama abin da ya kawo ni Ingila, amma rashin jirgi ya sa nake zaune a garin zuwa a bude hanya. Ina nan da rai na cikin koshin lafiya.

Daga nan sai ya godewa yan Najeriya bisa addu’o’in da suka rika yi masa. Sannan ya hori ‘yan Najeriya da su bi umarnin gwamnati da doka, sannan ya roki Allah ya kawo karshen matsalar da Jihar sa ta Kano ta fada ciki.

A yau ne jaridun Najeriya suka rika yadawa wai tsohon Kakakin majalisar tarayya Ghali Na’abba ya rasu.

Share.

game da Author