Idan mutane suka ci gaba da karya dokar Coronavirus zan sake garkame jihar – Gwamna Sanwo-Olu

0

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya nuna takaicin sa da rashin jin dadi kan yadda mutanen jihar ke karya dokar Coronavirus bayab an bude gari.

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa gwamnati za ta garkame jihar, ba shiga, ba fita idan mutane suka ci gaba da bijire wa dokar kiyaye wa daga kamuwa da cutar coronavirus.

Sanwo-Olu ya ce yadda mutane suke cakuduwa a kasuwanni da bankuna ya bani takaici domin. Sam mutane basu kiyaye ba ko kadan kuma ba za mu bari a cu gaba da haka ba.

” Idan mutane suka ci gaba da yi wa doka taurin kai, toh gwamnati za ta garkame jihar, kowa ya koma gida ya ci gaba da zama har sai an iya shawo kan yaduwar cutar a jihar.

“Gwamnati za ta dauki wannan tsautsauran matakai ne saboda kare kiwon lafiya da rayukan mutane a jihar.

Ya kuma ce gwamnati za ta dakatar da aiyukan masu motan haya da ‘yan acaba idan har suka ci gaba da saba wa dokar da aka saka.

” Saka takunkumin fuska da kiyaye sauran matakan samun kariya daga kamuwa da cutar ya zama dole a jihar.

Sanwo-Olu ya ce a cikin makonnin da za a shiga gwamnati za ta canja tsarin bude asibitocin kula da masu fama da cutar a jihar.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen bai wa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko damar kula da mutanen da cutar ba ta yi musu kamun mai tsanani ba musamman a yankuna karkara.

Mutum 1,780 suka kamu da cutar a jihar Legas.

Daga ciki 1184 na kwance a asibiti, an sallami 448, mutum 33 sun mutu.

Share.

game da Author