Har yanzu ‘yan sanda da mafarauta na neman Shugaban CAN da aka yi garkuwa da shi

0

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Bola Longe, ya shaida wa manema labarai a Lafiya cewa jami’an ‘yan sanda da dandazon mafarauta sun bazama neman inda mahara suka yi garkuwa da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), reshen Jihar Nasarawa, Joseph Masin.

Masu garkuwa sun arce da shi a ranar Alhamis tsakar dare, kuma har yanzu ba a ji duriyar inda suka boye shi ba.

An yi masa takakkiya har gidan sa da ke unguwar Bukan-Sidi, aka yi awon-gaba shi.

A kan haka ne kwamishinan na ‘yan sanda ya ce ya yi gagarimar gayyar gungun mafarauta a karkashin jagorancin wani gogarma.

Sun hadu da jami’an ‘yan sanda sun nausa farautar ‘yan bindigar da kuma limamin na daukacin Kiristocin Nasarawa.

Tsohon Sakataren CAN na Jihar Nasarawa, Yohanna Samari, ya kara tabbatar da sace shugaban na su mai matsayin Bishop.

Samari ya ce maharan da suka tsere da shi, a kan babura suka yi masa dirar-mikiya a gida.

Shi ma Mataimakin Shugaban CAN na Jihar Nasarawa Tayo Samuel, ya ce daga baya masu garkuwar sun tuntubi iyalan Bishop din, har suka nemi a biya kudin fansa zunzurutun naira milyan 20.

Ba a dai ji wa kowa ciwo ba a lokacin da aka tsere da shi.

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban CAN na neman naira milyan 20 kudin fansa

Share.

game da Author