Ministan kiwon Lafiyar Najeriya, Ehanire Osagie ya bayyana cewa haryanzu ba a samu wani hujja da ya nuna cewa mace-macen Kano daga annobar Coronavirus ne ba.
Minista Ehinare ya ce har yanzu ana bincike akan wadannan mace-mace a Kano kuma zaran an kammala za a bayyana abin da aka gano.
Idan ba a manta ba, jihar Kano ta yi fama da mace-macen mutane da dama, Malaman Jami’a, Sarakuna, manyan mutane da ‘yan jihar sun yi ta rasuwa a makonnin da suka wuce zuwa yanzu.
Sai dai sakamakon bincikin da aka yi na farko ya nuna cewa da yawa sun rasu ne a dalilin fama da suka yi da zazzabin cizon sauro da Sankarau.
Amma kuma Sani Gwarzo, Kodinaton Kwamitin dakile yaduwar Coronavirus, na jihar Kano ya bayyana wa Cable cewa cutar Coronavirus ne ya kashe mutane a Kano.
” Saboda haka idan mutane zasu farka daga barcin da suke yi su farka domin nan da sati daya ko kwanaki sakamakon binciken zai fito kowa zai gani wa kansa.
Jihar kano na da mutum sama da 300 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, sannan ita ce jiha ta biyu a yawan wadanda suka kamu da cutar.
A Najeriya mutum sama da 2000 sun kamu da cutar.
Discussion about this post