Daukacin Gwamnonin Najeriya 36, sun ki amincewa da Kudirin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa, wadda yanzu haka ake tafka kwatagwangwamar hayaniya saboda ita a Majalisar Tarayya.
Kudirin dokar mai suna ‘Control of Infectious Diseases Bill’, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi a Majalisa.
Duk da cewa bai samu na’am da karbuwa daga masu yawan mambobin majalisar ba, tuni kudorin har an yi masa karatu na biyu a zauren majalisa, kafin korafe-korafe, suka, caccaka su sa a dakatar da batun sa.
Yadda kudirin dokar ya yi nakin jini
Kafin Gwamnonin Najeriya su nuna rashin amincewa da kudirin, ‘yan Najeriya da dama da wasu ‘yan Majalisa duk sun nuna damuwa dangane da yadda ake ta gaggawa, azarbabi da rawar jikin hanzarta amincewa da kudirin.
Ana ta mamakin yadda a ranar da aka gabatar da kudirin yadda Shugaban Majalisa, Femi Gbajabiamila ya hakikice wajen amimcewa da kudirin, duk kuwa da cewa kusan gaba dayan ‘yan majalisar ko samun damar lokacin karanta kudirin mai babi 82 ba su yi ba.
Wannan kurman karatu da Gbajabiamila ya biya wa mambobi, ya haifar da rashin amimcewa daga ‘yan Najeriya masu bibiyar al’amurran yau da kullum.
Kudiri Ko Satar-fasaha?
An rika yin tir da cewa gaba dayan kudirin wankiya aka yi daga wata dokar kasar Singapore, wadda kasar ke amfani da ita wajen kokarin dalile cututtuka masu yaduwa.
Salon rubutu, Turancin da aka yi amfani da shi da kalmomin da ke cikin kudirin mai babi 82, an tabbatar da cewa duk satar-fasaha ce aka kwafo daga dokar Singapore.
Kungiyoyin kare hakkin jama’a kuma sun rika yin kururuwar cewa kudirin idan ya zama doka, to za ta takura kuma ta danne hakki tare da tirsasa wa ‘yan Najeriya yin abin da bai dace a tirsasi a karkashin mulkin dimokradiyya ba.
An kuma yi korafi a kan wani babi, wanda zai tilasta kowane mai fita kasashen waje da mai shigowa sai ya mallaki katin shaidar lafiyar sa garau. Wannan wani kati daban aka bijiro da shi a cikin kudirin, wanda ba ‘yelo card’ da matafiya suka sani ana amfani da shi ba.
Ba mu yarda da Kudirin ya zama doka ba -Gwamnonin Najeriya
Cikin takardar da Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal, Gwamnan Sokoto ya sa wa hannu, gwamonin su 36, sun ce sun ki amincewa da kudirin domin ba a tuntube su ba, a matsayin su na jagororin jama’ar da ake kokarin a kakaba wa dokar.
Sun kara da cewa ya kamata a nemi jin ra’ayin jama’a kafin a yi azarbabin yanke hukuncin neman a mayar da kudirin zuwa doka.
Sannan kuma Gwamnonin sun karta alamar tambaya dangane da karfin ikon tirsasa killace mutum da kuma tilasta yi masa allurar rigakafi da kudirin dokar ya bai wa Ministan Lafiya da Shugaban Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).
Gwamnonin sun ce tilas majalisa ta jingine kudirin. Sannan kuma sun nada gwamnonin Sokoto, Katsina da Filato su zauna su yi nazarin kudirin daga nan su zauna da shugabannin Majalisar Tarayya domin a sake tsefe gashin kan kudirin dokar gaba daya, ba don komai ba, suka ce don kada a yi wa ‘yan Najeriya kitso da kwarkwata.
Discussion about this post