Gwamnatin Tarayya ta aika wa Kano da tirelolin abinci 139

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta aika wa gwamnatin jihar Kano da tirelolin abince 139 domin rabawa talakawan jihar.

Ministan ayyukan jinkai Sadiya Farouk ta bayyana haka, ta na mai cewa an aika da Tireloli 10 na shinkafa, Tan 2,438 na masara, Tan 1,380 na gero millet da tan 900 na dawa. Tace wannan abinci za a raba wa akalla mutum 300,000 a Kano.

Minista Sadiyya ta ce an aika ta tireloli 110 kano a watan da Afrilu daga ofishin ta.

” Ina kira ga gwamna Ganduje ya rabawa wadanda aka aiko da wannan abinci domin su wato talakawa da masakai da tsofaffi da basu da halin ko wata hanyar samun abincin ci

Jihar kano ce ta fi fama da cutar Korona a Arewacin Najeria. Zuwa yanzu sama da mutum 700 sun kamu da cutar sannan 35 sun rasu.

” Zuwa 6 ga watan Mayu, akalla mutum 729,847 a Najeriya sun ji alat na kudi a wayoyin su daga gwamnatin tarayya daga shirin CCT. Sama da mutum 84,045 daga Kananan hukumomi 15 a jihar Kano suke.

A nashi jawabin, gwamna Ganduje ya jinjina wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa wannan kokari da yayi na agaza wa mutanen jihar Kano a wannan lokaci da aka garkame mutane.

” Sannan kuma ina so in shaida cewa ma’aikatar jinkai ta Kasa ta isar da sakon a cikin lokaci.

Share.

game da Author