Gwamnatin Jihar Adamawa na neman wani kansila ruwa a jallo, bisa zargin sa da hada kai da barayin shanu ana harkallar dabbobin da ake sacewa.
Sanarwar da ta fito daga Sakataren Gwamnati, Humwashi Wunosirou, ta bayyana cewa ana cigiyar Kansila Makama Enan Ngari mai wakiltar Mazabar Vulpi cikin Karamar Hukumar Numan, saboda hada baki da barayin shanu su ka yi wa masu dabbobi barna da harkallar cinikin dabbobi.
Sakataren Gwamnati ya ce ana cigiyar sa ganin yadda aka gano ya na maida hannun agogo baya, alhali gwamnati ta yi kokari ta maido da zaman lafiya a yankin, bayan hare-haren barayin shanu da fadace-fadace tsakanin makiyaya da mamoma, a yankin kan iyakar Jihar Adamawa da Taraba.
Ya ce gwamnati ba za ta sa ido wasu batagari na maida mata hannun-agogo baya ba, a wannan kokarin da ta ke yi ba kara wanzar da zaman lafiya a jihar Adamawa.
Ya yi kira ga al’ummar jihar au ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya wajen fallasa batagari. Sannan kuma ya yi gargadin cewa jama’a su daina daukar doka a hannun su.
Duk wani sabani, ya ce a bar hukumar da aikin hukunci ya rataya a kan ta, ita ce za ta zartas da hukunci.
Jihar Adamawa na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya, wadanda tashe-tashen hankula rikicin Boko Haram, ‘yan bindiga da na makiyaya da manona ya hana zaman lafiya.